Advertisement
Trending

Ma’aurata: Abunda Yakamata Ku Sani Game Da Jima’i

Ma'aurata: Abunda Yakamata Ku Sani Game Da Jima'i

TSAMMANIN DAKE ZUCIYOYIN MUTANE GAME DA JIMA’I A ZAMANIN YAU
●••••○•••••●•••••○•••••●•••••○•••••●••••

Bayani ne mai nauyin gaske da kuma ke kunshe da dunqulallun bayanai masu mahimmanci. kamar yadda na alkawarta abaya zanyi!

Toh saide da farko zan fara da cewa; gaskiya idan kasan ko kinsan bakya iya tsayawa ku karanta dogon post a natse komi mahimmancinsa toh ina rokonka dakai gaba kurum, domin post din me tsayi ne kwarai, ahakan ma na takaita shine bakuma nason rabashi saboda hakan zai iya sa wani parts din ya zamo missing… saika karancesa zaka fahimcesa da kyau….

Amma nayi BOLD HEADLINES da paragraph aciki da zaka iya fahimtar inda ka tsaya koda baka karancesa lokaci daya ba.

🌻🌻🌻

Hakika rayuwa da kuma zamani sun canza takai ga wasu abubuwan da ada ake lullu6esu ayau sun fito fili har sunfara zamowa bakomi ba. Da yawa mutane basu dauki tattaunawa game da irin wadannan ke6antattun al’amura na jima’i wani abu ba musamman atsakanin sa’oin juna, abokai ko kawaye maza da mata.

Mata basa jin kunya su zauna tsakaninsu ko wani group-group suna tattaunawa game da yadda mazajensu ke saduwa dasu, subahanallah. Haka ma cikin Mazan… duk da ansan wannan bai daga cikin tarbiya ta musulunci.

Toh saide nisara yacimu da yaki kuma dama Annabi ya fadamana inde muka daukesu ababen koyi toh Koda zina suka dawo yi agefen titi muma ana nan wataran sai mun fara jaraba hakan……

::::::::::::::::::::::~~~~~●~~~~~::::::::::::::::::

SHIN TAYA SUKA CIMU DA YAKIN ??

Anci mu da yaki ne ta hanyar kafofin internet da social media dake yaďa batsa da alfasha barkatai a waya📲 da mutum zai hau internet ya danna ya shiga shafin da duk yakeso ya kalla ko takalli duk irin abunda takeso na jima’i da rashin kyautawa, wanda kaso mafi yawa sun bude ido dasu ayau har kuwa da masu aure cikin masu bibiyar irin wadannan shafuka wanda hakan ya canza tunanin alumma daga fuskantar gaskiya zuwa karya.

Sannan kuma uwa uba ga group-group na batsa a social media da haka kurum yaro ko yarinya zasu zauna su tsara batsa zallah sui posting kaga wacce ko aure batai ba amma ta zage tana bayanin yadda ake kwanciya…
ko kuma bayani yadda kaza ya kasance tsakanin wane da budurwarsa wance haka kurum kirkirarrun labarai na banza da wofi da mutum me cikakken hankali bazai dauka ba…..

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Toh amma kasan dake kwakwalwa wawuyace, sannan wasu tunaninsu bai wuce saman gashin kansu… wadancan rubututtuka da suke karantawa tare da videos da suke kallah duk sai su aransu lallai fa hakan ce ta faru… don haka nima ya zanyi nai kaza dinnan ko kuwa in Mace ce ya akai mijina bai mun kaza dinnan gaskiya yana cutata kenan.

Wanda dalilin hakan kesa sakararru cikin Matasan mu su bazama neman maganin gaba batare dafa yaje wajen likita andubasa an tabbatar baida lfy ba! A’ah kurum shine tunda yaji anqaga labari kan abunda baya iyayi toh kurum ya lamincewa kansa dole yana da bukatar magani shima baida lfy…

Hakan yasa gashinan matasan mu shekara 20 zuwa 45 nata faman fankan-fankan suna shan magungunan hausa dana turawa alhalin lafiyarsu kalau, raina wuya sukai sukaje kaa adalilin kallo da karatun abubuwan da gidadancinsu ne ya kaisa garesu… karshe har shaye-shayen magungunan ya haddasa masa matsalar da ada bashi da itan.

Ko kuma wani kurum ya kawoma labarin maganin jima’i ka hau sha alhalin kalau kake kasani wai kai zakaiwa kanka service. Ai ba service sama da samun hutu, isashshen bacci da abinci me kyau. Abun haushi wasu nashan wadannan magungunan ne domin aikata zinace-zinace.

Hakama ciki MATA zakaga mace na zaune lafiya amma karatun batsa yasa ta fara ganin kasawar mijinta harta dena jin gamsuwar da take samu dashi, saboda taga video ko labarin da bakomi sai karya, rashin kangado da juya lafiyayyen tunani….Kaji ana anyima wata hawa yakai 3 zuwa 5 tana inzali kamar famfo….

Wanda kuma in ba’ai muwafaqa ba daga hakan mace tunda ta raina mijinta kome yai bazata gani ba don haka saita fara tunanin ina zata samu ta shigo da namiji wanda kafin a farga shikenan ta zama mazinaciya…

Kuma mafi illar intaji duk mazan basui daidai da curiosity din da ta karanta ba akarshe tana karanta labaran jima’i harda na madigo dan haka saita fara tunanin jarraba neman mace yar uwarta wanda ta wannan hanyar yau Allah kadai yasan matan auren da suke madigo. Za kaga Miji na can wajen neman halak, matarsa ta kawo ko ta tafi wajen wata na suna alfasha saboda iskanci da rashin ganin girma Allah da manzonsa.

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Don haka adalilin finafinai da posts na batsa da maza da mata ke ta ammali dasu yasa cikin mutanen mu duk sun raina lafiyar kansu alhalin kalau suke wanda hakan ke nuna kalle-kallen finafinan batasan da karanta labarurrukan batsa ya soma haddasa musu larurar kwakwalwa ta SEXUAL AVERSION DISORDER ko OCD wacce wataran inba Allah ya kiyaye ba tohfa bama kasa zama ko rike aure ba abunda zai sameku kila sai andaure mutum, domin zai shiga abubuwan da matar saita gudu…. Gashi nan Allah kadai yasan masu saduwa ta dubura kurum tsit matan suke, da masu turamusu abubuwa iri-iri a farji… kuma ana nan depression zai gama da mutum.

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Yaku Matasan mu Mata da Maza kusani finafinan batsa ba gaskiya bane. Fantasies ne kurum, wani girman size din gaban namiji da za’a nuna duk prosthesis ne kamar yadda suke hada Dildo suna halakar da matan mu ayau kaga sample din gaban namiji sak to suma hakan ake basu penis implant me laushin dake sajewa da fata wanda bazaku iya tantancewa ba kuzo kuna raina abunda Allah ya baku wanda a zahiri ma naku yafi nasu…

Haka nan maniyyin da zakuga ana fitarwa yana tsartuwa a irin wadannan clips din duk FAKE ne wallahi ba maniyyi bane na gaske… Kirkirarren solutions ne da ake hadawa da spunks da methilcellulose…

Sannan abunda ke faruwa yadda kuke ganin igiyar karin ruwa da ake sawa mara lafiya ahannu… haka ake zura wannan igiyar bututun ta cikin PENIS implant din ya biyo kasan matsematsin namijin ya saje da fata bazaku iya ganin ingiyar tube din ba… don haka me kwantrol din yana daga baya rike da katon siringi irin 60ml din ya zuqi kirkirarren farin maniyyi din iyakaci in sun nuna muku kamar anagama saduwa sai director din ya bada umarnin me rike syringe din ya danno maniyyin sai kuga abu yana tsartuwa ku dauka ajikinsa yake fita….

Wanda wannan abun shikesa wasu matan su rika ganin mijinsu kamar bashi da lafiya… ko shi namijin saboda sakarci ya rika wai baya fitar da ruwan maniyyi sosai ya raina kansa. Shiyasa galibi tambayar farko da nakewa irin wadannan in sunce mun wai suna da karancin ruwan mani itace ta ya kagane baka fitar da maniyyi sosai? Me ya nuna ma hakan? Ko kuma ma na share mutum…. domin akwai shirme kila mutum ya haihu ya qara yiwa mace ciki amma wai yana batun karancin maniyyi… kana da karancin maniyyin zaka iyama mace ciki? Da munji haka munsan inda ka samo wannan tunanin…

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Sannan MATA babu wani abu wai shi Release a mace da kuke gani ana haska muku ko kuke karantawa a posts marasa tsafta wai mace ta kawo tana tsartuwa maniyyinta kamar zai ta6o saman ceiling daki…😊 Karyar banza ce.
Abunda ake nufi da Orgasm din mace shine gamsuwar ita akaran kanta ne aranta cikin kwakwalwarta zataji ta gamsu kuma intai irin wannan jikinta ne mneke saki kamar yadda namiji inyai inzali zaiji sha’awa ta qare masa….

Akwai wani abu daga cikin cuttukan jima’i da ake kira UROPHILIA wanda abokin jima’i ke sha’awa yin fitsari jikin daya yayin jima’i abunda kan samesu kenan ku rika zaton maniyyi mace ke fitarwa fitsari ne.. sai kuma irin Artificial lubricates da ake samusu ta syringe suma adanna ku zaci wai release suke.

Za aima yara aure kaji mace tazo tana ita de tana saduwa amma bata ta6a ganin tai release ba… inajin wannan suma nasan inda suka dauko wannan gurbataccen tunanin… karatun post din batsa ne. Eh gaban mace yakan jike yai damshi saboda glands amma babu wani abu wai Release ko inzali a mata. Don haka kaima sakaran namiji dake jiran wai kaga matarka tai release kasani babu wannan abun baza kuma ka ta6a gani ba.
~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Sannan sakamakon ganin irin wadancan abubuwa na girman size din azzakarin porn stars sai kaji namiji yazoma wai yana fama da kankantar gaba. Shi gabansa ba tsayi, wanda galibi inka binkicesu normal size garesu… kurum low self esteem ne ke damunsu. Eh anji wani azzakarinsa yafi na wani tsayi da kauri amma hakan bashike nuna kaima naka yana da matsala ba….

Sannan mutum xaizo yana takaici duk depression ya damesa wai baya iya jimawa a jima’i minti 5 yake kawowa… kuma gashi lafiya kalau rayuwar aurensa yana da sha’awa wanda abunda ke nunawa shine kila mutum ya kasance mai kallon finafinan batsa yana ganin video na minti 10 zuwa 40 ko sama duk kuma a nuna mutum daya ke jima’i. Don haka shi mai yin minti 5 sai ya fara sawa ransa cewa lallai toh baida lafiya.

Wanda kuma nafada muku duk karyace wancan videon babu wani jima’i irin wannan kamar yadda nace muku delusion ne ku kuke ganin jima’i amma ba gaskiya bane kaso 60% na abunda kuke gani FAKE ne.

Abunda nakeso kusani eh akwai wasu larurorin dake hana samun sha’awa kamar karancin sinadaran jima’i, larurar kunci da fargaba wato anxiety/depression. Sannan musamman depression yana iya haddasa saurin inzali,

Haka kuma inde halinka ne masturbation toh dama ka qulla abota da saurin inzali, inkai wasa ko kafin kake cire kayanka zaka iya kawowa ma kan ka ta6a macen domin ka birkita kwakwalwarka ta yadda tuni take fara jima’in kafin jikinka ya fara… kuma shyasa ko aure sukai suke samun matsala.

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Sannan wani girman breast da kuke gani a irin wadannan finafinan duk SILICONE implant ne ba NATURAL bane aiki ake asamusu, shaysa har cikin maza transgender wato yan daudu cikin turawa suma zakuke ganinsu da nonuwa…

Inkace wai kayi amarya kuma haka kake tsammani kaga mace budurwa irin tamu da irin wannan nonon na video toh a gaskiya ina jajantama domin ka HAUKACE.

Eh mana hauka ya fara samunka kuma wannan tasa sai mutum ya hau zarge zargen banza yana ganin kamar ba cikakkiyar mace ya aura ba saboda gurbacewar tunanin da ya shafe shekaru kimanin 2 zuwa 10 yana samu na kallon batsa. Bawan Allah ba haka abun yake ba. Duk FAKE ne

Sannan dan mace budurwa ce baya nufin dole nono bazai rusuna ba. Me ka fahimta da tsayawar nono ne? Ko yadda suke cikin rigar nono kace haka kake tsammanin ganinsu a zahiri ka yaudari kanka ballantana na wasu can da duk FAKE ne. Kuma ko mace ce kikace sai kin zama irin wadannan toh aiki ya ganki suma ba natural bane.

Matasan mu ku cire wannan tunanin ku rike iyalanku da mutunci iyakarsu kenan kuma sunfi wadancan a zahiri.

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

WANI ABUN TAUSAYI

Ko kasan irin wadannan matan na porn industry ko kaga suna dariya kuka da nadama ne akasan zuciyarsu galibi yaudaro su ake a satosu asakasu cikin wannan harkar.
Daga wata kasa ake ketarowa dasu Bodojin kasa ashiga dasu wata kasar… da sunan za’a sama musu aiki da zasuke dibar albashi me tsoka karshe akawosu harkar fasikancin duk abunda kaga sunyi a irin wannan finafinai dole ake musu har karshe dattin zinar ya shigesu ya zame musu jiki…

Wasu iyayensu suna can sunyi kuka har sun gaji, sun cire rai dasu basu san inda suke ba. kamar yadda ayau ga kungiyoyi nan na qara yawaita na dibar musamman mata ayyuka zuwa kasashen waje har a irin kasashen toh galibi daga haka ake saida su ga irin wadancan mutanen fasikai sukuma sasu a pornography….saboda duk wanda ya shiga ya kalla kudade suke samu….

Toh ya zakaji don Allah ace ga mace yar kasarku ko yar jiharku ana haskata a irin wannan ana cin zarafinta… kaga inda kunsan gaskiyar pornography wlh bai kamata ku tsaya kallo ba domin yayan wasu ne ake cin zarafinsu kuma ko basaso sai sun kwanta da namiji akalla wata 7 arana wasu… saboda masu irin wadannan kamfanonin suna da daurin gindi.

Don haka ku kiyayi irin wadannan shafukan ba mutuncin ku bane, ba mutuncin addinin ku bane… zaka gansu sunzo mana asibiti babu boyeboye aikinsu ne zasuita fadama sirrin rayuwarsu gwanin ban tausayi wasu har karaya suke samu agadon bayansu saboda Pose din da ake basu suyi wajen jima’i

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Don haka kamar yadda nake ta maimaitawa batun jima’i kusani duk abubuwan da kuke gani kuke karantawa ba gaskiya bane.

Kuma hatta masu rubuta batsa da hausa ku kiyayesu, kaga mutum ya dage ya qaga karyar banza da wofi matanmu sun karanta sun hau kai sun zauna.

Domin Taya mutum zai inzali kuma wai ko minti 2 ba aiba arubutun sai kaji ance ya qara daukar sabon caji ya kamota ankuma kaza da kaza… rubutu na rashin hankali da tunani…. haba jama’a

Malam ko bacci ka farko baka isa ka fita da gudu ba batare da ka fara tashi ka bude ido ka zauna kafin kai mika daga bisani ka mike ba… Haka baka isa ka bude laptop ko wayar da take kashe ba kurum ka fara aiki dole kajira saita Gama booting da loading…… toh kamar haka ne, baka isa kai jima’i kai inzali ba wai ka kamowa mace nan da nan karya ne.

Dole akwai abunda muke kira REFECTORY PERIOD da sai jikin mutum ya qara tattara sha’awarsa.. bazai yiwu ba ya koma jima’i nan da nan.

Amma a irin rubututtukan banzan nan sai kaji anyi jima’i hawa 3 zuwa 4 kuma duk lokaci guda… shikenan mutanen mu sun hau kai, inyaje ya kasa haka ya fara zargin baida lafiya, in macece mijinta ya kasa tafara zargin baida lafiya inbata da tsoron Allah kamar yadda nace karshe ta fara tunanin fara neman maza….

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Gashinan matasan mu lafiyarsu kalau amma sun haikewa amafani da magungunan jima’i… sai samun cuttukan zuciya suke basu sani ba ahankali, da anyi hatsari sun bugu da karfi shikenan mutum kaga ya mutu. Ai hatsari kaga dattawa sun haure matasa kwance sun zama gawa tunda magunguna ne ba irin paracetamol ba su kwakwalwa suke firings….

Suma matan rashin hankali mace na zaune kalau saita hau zargin wai ta bude… bari tai amfani da maganin matsi karshe hakan yaita qara zuge gaban mijinta shi kuma sakarai yana bude baki a matse take alhalin shi akewa illar

Domin abunda baku sani ba shine; gaban namiji in jini bai tsirgawa wadannan jijiyoyin jinin ba sun cika, gabansa bazai taba mikewa ba… toh duk sanda kika takure gabanki da sunan matsi da kyar zai shiga kuma inya shiga jijiyoyin azzakrinsa matsewa zasui don haka nan danan gabansa zai sanyi yaji kamar ana tsotsarsa yai release ya fita alhalin ke baki ma fara jin dadin Jima’in ka’in da na’in ba… karshe kina kashesa, kina kuma cutar kanki don haka karshe kekuma zakije inda matsin bazai aiki ba duk tsokokinki sun gama contracting dole ko baida hali ya fara wuniwunin karo aurr karshe matsi ya jawo miki abunda kike gudu.

Ko anfadamuku bakwaji shyasa gakunan kuke kashe mazajen naku da kanku amma ku rika zaman hira mijinku baya iya kaza da kaza….

Haihuwa da kuma tsufa in shekaru sun haura 45 zuwa 50 shine ke bude farji kamar yadda nake fada muku…. inba haka ba babu wani abun dake bude farji… saide in macen dake da abokanan saduwa barkatai nasha fadamuku… toh me yai zafi banda shirme kina budurwa ko ke da haihuwarki batafi 3 ba ki rika sa kanki a irin wannan hali.

~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~

Don haka inbaku dena ba kuma mazaje sukaci gaba da shayeshayen magungunan karin karfi toh ko baka mutu da ciwon zuciya ba zaka hadu da shanyewar 6arin jiki.. wanda wannan abune da ya fara faruwa… gashinan yan dan shekara 20 sai kagansa da STROKE ayanzu wanda ada sai dan shekara 60 zuwa 70.

Sannan galibi matasan mu suna da hawan jini amma dake silent killer ne basajin alamu ahaka kuma suke haikewa wadannan magungunan arashin sanin illarsu domin kurum mutum chemist zaije yace abashi, shiko mai chemist ko pharmacy kudi yake nema… wanda duk shan maganin karin chance ne na mutuwa adalilin ciwon zuciya ko shanyewar jiki. Domin ko haka lafiya duk sanda kazo jima’i Bp dinka yana karuwa, bugun zuciya ma karuwa yake ballantana ka qara da kwaya wasu shikesa suna fasikanci asamesu sun mutu adakin hotel saboda cardiac arrest.

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

KANKANTAR AZZAKARI

Kusani mafi kankantar tsayin azzakarin da inkana da kasa dashi shine zaka zargin kanka da kankantar gaba shine inya gaza kaiwa 5.1 zuwa 5.6 inches wato 12.9cm zuwa 14.2cm sanda ya mike….
Wasu gabansu sukan ganshi karami amma ba anan abun yake ba… galibi inya mike normal size ne don haka baka da bukatar ka dami kanka… Sannan akwai lokuta musamman na sanyi azzakari yakan 6oye kansa ciki saboda tempreture….

🚥
Sannan in ance tsayin azzakari wasu sun dauka kurum iya inda zuke iya gani da ido daga dan gashin gaban nan nasu zuwa wajen fitar fitsari nan ne tsayin azzakari! Kuskurene ai wannan da kake gani baifi rabin tsayinsa. Inkanason sanin tsayin gabanka toh tundaga can kasan tushen yayan marainanka daf da dubura inkabi zakaji nan ne tushensa inda ya somo… wato Groins Area toh daga nan ake fara auno tsayin azzakari bawai daga iya wajen gashin gaba ba… shyasa da wuya kayi kaga ya gaza 13 centimeters…

Ka gwada sa zare ka auno daga can inya mike tundaga tushen inyazo saika sami doguwar RULER ka auna tsayin zaren na abunda ka samu ajikin CM ko Inches na ruler din anan zaka gane tsayin gabanka inma kana da matsala ko babu bawai abunda kake gani a video ba.

🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥🚥

SANNAN GAME DA TSAYIN JIMA’I

Kamar yadda nace zaka ke cin karo da maganganu marasa tsafta, da sunan ana koyama mace yadda ake saduwa, gamsar da maigida, koya kwanciya ko kuma ka rika Jin labarai na batsa akan yadda wane ya kwanta da wance; cewa ya kwanta da wance bayan yai release, ya kuma kamota yaci gaba da kaza da kaza, suka kuma release atare, ya kara komawa kaza. Akarshe de sai kaji de adan wannan lokacin ana nunawa masu karantu namiji yai release 3 zuwa 5 ko 6, ya shafe sama da awa 1 ko 2 yana jima’i.

Toh Wallahi ba irin wannan jima’in cikin mutane saide ko aljanu bansani ba. Na rantse domin zuciyar ku ta sami nutsuwa saboda yara ne ake aurar dasu yanzu wadanda idonsu ya bude da irin wadannan zantuttukan saboda haka zarar hakan bata faruwa sai’su fara tunanin mazajensu basu da lafiya, tare da fara turo tambayoyi bayan kagagen yasashshen zancene kurum da suka saba ji ya jawo haka.

Wallahi mazajen mu da yawa lafiya kuke saide dan abunda ba’a rasa ba na rashin iya wasa yadda zakuke samun gamsuwa atare.

DOLE AKWAI REFRACTORY PERIOD KAMAR YADDA NACE

Refrectory shine lokacin da jiki zai qara tattara sha’awa wannan ko ya bambanta daga mutum zuwa mutum; wani bayan minti 15 zai iya komawa musamman inyana da karfin sha’awa da yawa, wani minti 30, wani awa 1, wani 3 wani awa 12 ma sannan wani kuma kwana 1 ma,
Kuma hakan bai nuna mutum bashi da lafiya ya danganta da halittar jikinsa,

Saide eh akan samu masu larura musamman idan megida yana da hawan jini ko ciwon suga musamman ciwon sugar kuma ciwon ya jima ajika ya dole wannan matansu sai hakuri domin ciwon bai barin su sami mikewar gaba domin Diabetes na lalata jijiyoyi sosai musamman inba a kiyayewa sosai. Don haka magance sugar da hawan jinin shine mahimmi ba shaye shayen maganin jima’i

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

SHIN YA JIMA’IN MA YAKE

Yawan jima’i na cutar da jiki, don haka tazarar kwana 3 Kän zama normal matukar Ana samun tazarar awa 72 kwana 3 shi kansa sinadarin sperm hakn zaisa ya zamto mai karfi da lafiyar da ciki zai iya shiga nan da nan, bawai kullum kullum ba.

1]■ A bisa binkicen masana kusantar kanta Kän fara zama kusanta ne daga zarar ansami secons talatin da uku (33secs).

2]■ Mafi kankantar jima’i a ilmance shine wanda yake farawa ya kare iya minti daya zuwa biyu. Toh kaga me tunanin minti biyar bashi da lafiya saika canza tunani

3]■Matsakaici Kuma gamsashen jima’i….
bai wuce minti bakwai da secons 4 hade da wasanni dakan tada sha’awa wanda bai wuce na minti 2, saboda haka Inka cire minti 2 cikin 7 saura biyar da secons Arba’in (5.4minutes) wannan 5.4minute shine normal duration da akan dauka dan haka ba daidaine minti biyar ace namijin baida lafiya ba illa de ya dage da service din kansa domin kamar inji ne dole Saida service.

Allah Yasa Mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button