Advertisement

Amfanin Aya Mai Nono Agun Mace Marar Nono

Mai karatu barka da wannan lokaci, mu na fatan ka na cikin koshin lafiya, ALLAH YA sa haka amin. A makon da ya gabata mun kawo mu ku makala kan amfanin ganyen magarya wacce mu ka yi wa taken,

A wannan makon za mu kawo mu ku amfanin da AYA ke da shi ga lafiyarmu.  Da harshen Hausa mu na kiran ta AYA, yayin da Turawa ke kiran ta da “Tigernut”. Kafin tsunduma cikin makalar, kamar yadda mu ka saba wannan karon ma, za mu kawo mu ku irin tarin sanadaran da aya ke kunshe da su.

Daga cikin irin tarin sanadaran da aya ke kunshe da su akwai, sanadaran magnesium, calcium, iron, nau’ikan Vitamins daban-daban, protein da sauran su. Wadannan sanadarai da aya ke da su, na da matukar muhimmanci wajen inganta lafiyarmu.

Binciken kimiyya ya nuna wadannan sanadarai da aya ke kunshe da su na inganta lafiyar jikin bil’adama, sa na samar da kuzari da karin nishadi da sha’awa ga ma’aurata. Baya ga haka ana hada magunguna da dama, misali wani bincike ya nuna cewa, man aya dai dai yake da man zaitun wajen samar da magani.

 

Ba tare da cika ku da karin bayani ba, ga jerin irin magunguna da aya ke da su ga lafiyar dan adam. Da fatan Allah Ya sa mu dace, da kuma fatan a sha karatu lafiya.

1.  Aya Na Gina Jiki Cikin Gaggawa.

Sanin sirrin da ke tattare da aya da masana ke da shi sakamakon zuzzurfan bincike da aka gudanar kanta, ya sanya ake amfani da aya wajen gina jiki. Wannan dalili ya sa ake amfani da aya a yankunan dake fama da karancin abinci mai gina jiki. Ana amfani da aya wajen inganta kiwon lafiya ga ma su fama da karancin abinci mai gina jiki sakamakon yawan sanadarai ma su matukar amfani ga jiki da aya ke kunshe da su, kamar sanadaran carbohydrate,magnesium, phosphorus, iron, fiber calcium, sodium, copper, iron da kuma zinc.

2.  Maganin Matsalolin Ciki.

Aya na da matukar fa’ida wajen maganin matsaloli da kan shafi ciki. Ba don komai aya ke taka wannan muhimmiyar rawa kan matsalolin ciki ba, sai dai sakamakon wasu sanadarai da ta ke dauke da su, dake inganta wa tare da magance matsalolin ciki musamman wadanda su ka shafi hanji. Sakamakon haka ta ke taimakawa wajen maganin cushewa da kumburin ciki.

 

3.  Gyaran Jiki.

A nan idan ana maganar gyaran jiki mu na nufin inganta lafiyar jiki da suka hada da gyaran fata, gudanuwar jini, kuzarin jiki da sauran su. Yawan sanadaran gina jiki da aya ke da su ya sa ake amfani da ita wajen gyaran jiki, sakamakon haka ta ke gyara fata ta koma kamar ta yaro, ke nan ta zama “Mai da tsohuwa yarinya”. Baya ga haka ta na karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzarin jiki.

4.  Kara Qibar Jiki.

Aya na taimakawa wajen karawa mutum kiba cikin sauki. Domin samun wannan fa’ida sai a samu aya mai kyau, a daka ta, daga nan sai a zuba ta cikin ruwa ta kwana, idan gari ya waye, sai a  tace a zuba sikari a shanye. Haka za a juri yi. Cikin yardar Allah ramar da mutum ke fama da ita za ta gushe ba da jimawa ba.

Gantaa yuwar Aure.

Ba shakka bincike ya nuna yadda aya ke inganta rayuwar aure. Idan mu ka ce rayuwar aure, mai karatu zai gane inda mu ka dosa. Dalili anan shine ta na kara dankon soyayyar ma’aurata ta hanyar taimaka mu su wajen gamsar da junansu a lokacin jima’i. Ba don komai ba sai don amfanin ta wajen kara yawan ruwan maniyyi, sannan ta na karawa mata ni’ima da jin dadi yayin saduwar aure.

6.   Kara Ruwan Nono Ga Mata.

Aya na da matukar amfani ga mata ma su shayarwa da ke fuskantar rashin ruwan mama.  Saboda haka duk mace mai shayarwa dake fama da wannan matsala ta karancin ruwan nono sai ta dimanci amfani da aya.

7.  Kara Karfin Garkuwar Jiki.

Aya na da sanadaran dake taimakawa wajen inganta garkuwarmu, kuma mai karatu ya san cewa, duk lokacin da garkuwarka ta zama mai karfi, to a lokacin ne za ta iya yaki da cututtuka da kan kai wa jikinka farmaki.  Saboda haka ne ya sa aya ke iya yin fito na fito da kwayoyin cuta da za su iya illata jikin dan adam.

8.  Aya ta na inganta lafiyar Ido sannan ta na kare mutum daga kamuwa da cututtukan ido.

9. Aya na samar da maganin tsutsar ciki.

10. Aya na taimakawa wajen daidaita kewayawar jini a jikin bil’adama.

11. Aya na taimakawa wajen narkar da abinci.

12. Ta na kare mutum daga hadarin kamuwa da ciwon mafitsara.

13. Aya na rage wa mutum hadarin kamuwa da ciwon zuciya.

14. Aya na rigakafin kamuwa daga cutar hanta.

15. Hakanan Aya na taimakawa wajen rage kitsen cikin jini marar amfani a jikinmu.

16. Aya na magance matsalolin fata kamar su kezbi, kora, makero, pinpus da sauran su.

17. Aya na taimakawa wajen samun kuzari

Ana kiran wannan itaciya da goruba a harshen Hausa, da turanci kuma ana kiranta da ‘Doum palm tree’ yayin da suke kiran &#…

A wannan makala za mu kawo muku yadda za ku kara girman azzakarinku, idan mu ka ce girman azzakari mu na nufi, kauri da tsawon azzak..

Ko mai karatu ya san irin sanadaran da lemon tsami ke kunshe da su ? Kuma ko ka san amfaninsa ga lafiyarmu ? Idan ba ka sani ba, mu …

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda ya yiwa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a babban zaben kasar nan na 2019

‘Yan sanda a jihar Oyo sun kama wasu mutane hudu da ake zargi da safarar makamai ba bisa ka’ida ba tare da tarin alburusai da …

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button