Advertisement
Trending

Amfanin Namiji Goro Guda Goma (10) Da Ya Kamata Kusani Harda Bangaren Ma’aurata

Amfanin Namiji Goro Guda Goma (10) Da Ya Kamata Kusani Harda Bangaren Ma'aurata

NAMIJIN GORO DA AMFANIN SA

A nazarin da aka gudanar
daban-daban a Africa dama Turai, Masana kiwon lafiya sun bayyana Namijin Goro yana dauke da sinadarai masu yaki da cututtuka da dama dake jikin nmutum. Sun tabbatar Namijin Goro yana da amfani kamar haka:

1) MAGANIN TARI DA CIWAN
SANYI: Namijin Goro yana maganin kusan dukkan cututukan sanyi na kirji(chest cold). Kamar yawan tari, atishawa, cutukan makogaro, toshewar hanci, ciwan kai nagefe daya da cutukan bututun iska.

2) MAGANIN CIWAN IDO DA
KARA HASKAN IDO: Namijin Goro yana tai makawa wajan kashe cutar “Glaucoma” wadda take lalata idanun mutu.

3) MAGANIN CANCER, DIABETES DA HEPATITIS: Namijin Goro yana dauke da sinadarin “antioxidant” mai taimakawa wagen yakar cutar cancer da diabetes. Hakazalika yanada amfani
gamai cutar “hepatitis” dan yana da sinadarin yaki da cutar.

4) MAGANIN CIWAN JIKI DA
GABOBI: Namijin Goro yana bada kariya ga garkuwar jiki, akan hakanema masu ilinmin hada magani ke amfani da garinsa wajen bada magungunan yaki da cutar HIV, AIDS da Ebola tahanyar rage radadin gubar da cutar take dashi saboda sinadarin “Anticbacterial” da kuma chemical na “Saponin” daya ke ciki.

5) MAGANIN HANTA: Namijin Goro yana taimakawa wajan yakar cutar matsalar hanta (liver disorder).

6) NAKAR DA ABINCI DA TSEDA GUDAWA: Namijin Goro yana taimakawa wajan saurin narkar da abinci. Idan ciki ya kume, ko anci abinci mara kyau ko abinda idan anci zaibata ciki sai a tamna namijin goro, zaitaimaka wajan narkar da abincin dagaggawa batare da cikin yabaciba. Hakazalika yanada sinadarin dake taimakawa wajan tseda guduwa.

7) MAGANIN ZAZZABIN: Cin Namijin Goro yana taimakawa mutuka wajan magance kwayar cutar “malaria” saboda yana dauke da sinadarin “kolaviron” dake ciki mai kashe kwayar cutar. Kuma yana mutukar taimakawa wajan yaki da cutar zazzabin TYphold da Flu.

8) HANA KIBA DA RAGE KIBA: Namijin Goro yana hana jin yinwa, kuma yana taimakawa wajan rage yinwa tayadda baza a damu ba, yana saka yawan shanruwa, adalilin wannan kuma zakarasa kiba.

9) YANA WAKIN MARA DA
KARA KARFIN JIMA: Namijin Goro yana taimawa waje wanke mara, kuma ba abarsa abaya ba wajen karawa ma’aurata karfi, sha’awa da gamsuwa wajen jima’i.

10) NAWA_YAKAMATA A CI Abincikan da Masana kiwan lafiya suka gudanar sunyiwa Namijin Goro karin
magana(proverb) akan “Namijin Goro Guda Biyu A Rana Zaihanaka Zuwa Wajan Likita”.

Awani bincikan kuma masanan sunce namijin goro daya shine yafi dacewa da lafiya. WNannan itace ka’idar da zata taimakawa lafiya kuma bazata cutar ba. Kar aci Namijin Goro deyawa
alokaci guda ko a rana, dan zaihafar da matsala ga lafiya. Cinsa deyewa alokaci guda ko a rana, yana kawo matsala. Alura!. #shawarata :. ldan akasiya Namijin Goro, idan babbane arabasa gida 3, aci daya da safe, daya da rana, daya da daddare. Idan kuma karamine arabasa gida 2, rabi da safe, rabi da rana, da daddare kuma sai asamu makamancin sa aci.

Wannan hadin yanada mutukar amfani kuma bayasa damuwa dan mungwada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button