Advertisement

Yadda ake hadin maganin karfin gaba da ruwan citta domin gamsar da iyali

Yadda ake hadin maganin karfin gaba da ruwan citta domin gamsar da iyali

Kamar yadda bincike na masana ya nuna, citta tana daga cikin kayayyakin kara kamshi da dandano na abinci, inda amfanin ta bai tsaya anan ba, domin kuwa komai dake jikin citta yana da nasa amfanin tun daga bada kariya har zuwa waraka ga jinyoyi da ciwo daban daban.

Sannan dumbin maganin da citta take a jikin dan adam yasa ake sarrafata ta hanyoyi da dama, kama daga kan ciwon sanyi da mura ko kuma tari, har zuwa ga gyaran jiki da fata domin bayyana da cikar kyau da mutum yake da ita.

Citta ana sarrafa ta ta hanyar matsewa da kuma amfani da ruwan jikin ta wajen gyaran azzakarin namiji, musamman wanda ya kasance ba shi da karfi sosai a lokacin da yake yin jima’i da mace.

Wannan dalilin yasa mu kaga ya dace mu bayyanawa wadanda suke bibiyar mu ta wannan kafa hanyar da zasu samu damar rabuwa da damuwar su a bangaren daya shafi al’aurar su, ba don komai ba illa bisa dalilin ganin sun biyawa iyalansu bukata tare da gamsar dasu.

Akwai muhimman abubuwan da ake bukata wajen yin wannan hadi, sune suka hadar da:

– Citta (Gari ko kuma danya)
-Zuma (Original)
– Madara( Ta Ruwa ko Gari.
– Man kustulhindi.

Ana hada su kamar haka:

A samu Madarar mai kyau yar waje ko peak milk da sauran madara dai mai kyau, za’a tsiyaya ruwan chitta ko garin citta daidai misali. Sai a samu garin Kustul Hindi cokali daya a zuba aciki, daga nan se a sanya zuma daidai Misali se a shanye hadin duka, Minti 30 kafin kwanciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button