Sirri na musamman da ya kamata ko wacce mace ta sani domin biyawa mijinta bukata yayin saduwa

Sirri na musamman da ya kamata ko wacce mace ta sani domin biyawa mijinta bukata yayin saduwa

Hakika namiji yana da wani sirrin wanda ba kowacce Mace ta san wadannan sirrin ba sai wacce Allah ya sanar da ita, shi Namiji ya kasance mai tsanani son karairaya, rangwada, kissa, shagwaba, da kalaman soyayya, duk macen data san wadannan kuma take aikatasu hakika zata zama tauraruwa a zuciyar Mijinta.

Babu ko shakka wadannan kam na daga cikin abubuwa mafi muhimmanci dake taka muhimmiyar rawa wajen sace zuciyar Namiji, ya kasance kin tanadi wani suna na musamman da zaki dinga kiran Mijinki da shi kamar haka.

(1) Sweety

(2) Honey

(3) Darling

(4) Farin cikin rai na

Magana ta gaskiya a wannan fannin a nan ne aka yiwa Matan hausawa nisa, don da yawa sune basu dauki hakan a wani abu mai muhimmanci dake iya jefa tsantsar sonki a zuciyar Mijin ki ba.

Dole a matsayin ki na Macen dake son ta mallaki Mijinta saifa ta dage wajen iya kalaman soyayya don sune masu kwantarwa da Namiji hankali koda kuwa an bata masa rai ko hankalinsa ya tashi.

Sannnan yana daga cikin Namiji ki iya gabatar da zahirin soyayya, hakika tsakaninki da Mijinki bafa jin kunya ki saki jikinki ki nuna masa soyayya, domin duk wani hade-hade da manne-manne da zakiyi idan har baki iya kalaman soyayya ba da ita kanta soyayyar to gaskiya da sauranki.

Misali idan ya kasance ku biyu ne akayi sa’a baki iyaba ko kuma kice kina jin kunya amma ita abokiyar zamanki ta iya sai kiga yana zumudi a duk lokacin da akace yaune ranar kwananta.

Don haka dole sai kin dage kin jajirce kin iya salo-salo na soyayya.

Sannan daga cikin sirrin Namiji a wajen jima’i karki zauna shirim baki tabuka komai, ya kasance kema kanki kina gabatar da salo na shagwaba da duk wani yanayi da zai iya saki nuna masa cewa kefa kina jin dadin wannan jima’i dashi.

Abin da ya kamata kuyi ‘yan uwa Mata wadannan hanyoyin da muka kawo muku sune wanda zakuyi amfani dasu domin jan hankalin Mazajenku, domin jin dadin zamantakewar auren ku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button