Amfanin Hulba Ajikin Mutum Musamman Wanda Maniyyinsa Take Tsinkewa

tabbatar da cewa, yawan yin amfani da hulba cikin abinci na kara inganta lafiyar koda, ta hanyar sabunta kwayoyin halittar kodar, da hana su lalacewa.

 

 

9. Hulba na karewa hanta daga cutuka; Yawan amfani da hulba na taimakawa wajen karewa hanta daga kamuwa daga cutuka. Masana sun ce, hulba na wannan aiki ne ta hanyar fitar da sanadarai ma su guba, da ka iya yin lahani ga hanta.

 

 

 

10. Amfani da hulba na taimakon ma su fama da ciwon siga; An gano cewa, yin amfani da hulba na taimakawa ma su fama da larurar ciwon siga. Masana sun ce, hulba na wannan aiki ne, ta hanyar daidaita sigan dake cikin jini.

 

 

 

11. Hulba na taimakawa wajen sha’awar cin abinci; Ana amfani da hulba wajen magance matsalar rashin cin abinci. Idan mutum na fama da rashin sha’awar cin abinci, sai ya samu man hulba ya hada da zuma ya ke shan babban cokali 2 sau uku a rana.

 

 

12. Ana amfani da hulba don karin kiba; Wannan ba zai zo wa mai karatu da mamaki ba, idan ya yi la’akari da yadda mu ka bayyana a sama cewa, hulbar na taimakawa wajen sha’awar cin abinci, mun san kuwa cin abinci na da kyakkyawar alaka da samun kibar jiki. Saboda haka, mutanen da ke fama da matsalar rama, sakamakon murmurewa daga wata rashin lafiya za su iya amfani da hulba don samu waraka. Kuma za su iya amfani da hadin da mu ka fada a sama, kan karin cin abinci don wannan fa’ida.

 

 

Sai dai, wani tsokaci anan shine, mai son yin amfani da hulba don karin kiba, akwai bukatar bayan amfani da hulbar ya hada da cin abinci mai Gina jiki, kamar wake da dankalin turawa,da kifi da sauran su, don kuwa hausawa na cewa, ko da kana da kyau ka kara da wanka, kuma ko ba komai wadannan dangin abinci za su taimaka wajen kara wa jikinka karfi. Baya ga haka kuma sai ka guji cin nau’ikan abinci ma su maiko sosai.

 

 

13. Hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon daji; Ba shakka hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon dajin mama, musamman ga mata ma su shayarwa. Bincike ya nuna cewa, matukar mace mai shayarwa ta juri yin amfani da hulba, baya ga kara ma ta lafiya tare da jaririnta, hulba na ba ta kariyar kamuwa daga ciwon dajin mama (Breast cancer).

 

 

14. Ana amfani da hulba don maganin ciwon tari da mura da kuma sauran ciwon sanyi da kan shafi makogwaro.

15. Hakanan, za ka iya amfani da hulba don maganin zafin jiki.

16. Hulba na taimakawa wajen samun lafiyar ciki, ta hanyar maganin matsalolin ciki.

17. Mata na iya yin amfani da hulba don daidaita jinin al’ada ga matan da jinin ke mu su wasa.

 

 

18. Ana amfani da hulba don maganin kaikayin gaba; Yadda za a yi shine, A samu hulba a hada da gishiri a dafa sannan a jira ya huce yadda ba zai yi lahani ga jiki ba, sai a zauna a ciki, zuwa wani lokaci, a kalla dai a samu minti 30 a cikin wannan ruwan hulba. Haka za a yi har a samu waraka. Idan kina bukata za ki iya hada shayin hulbar ki na sha, ko kuma bayan kin dafa da gishirin, bayan kin debi ruwan da za ki zauna sai ki rage wani, ki jefa tsamiya ki sha.

 

 

19. Hulba na taimakawa mata dake fama da bushewar gaba; Ga matan dake fama da matsalar bushewar gaba, sai su samu man ridi su ke zubawa a cikin ruwan dumi su ke zauna wa a ciki, sannan daga bisani sai su ke yin matsi da Hulba, insha Allahu za a dace.

20. Hulba na maganin ciwon ciki bayan haihuwa

 

 

21. Ana amfani da hulba don gyaran nono; Bincike ya tabbatar da cewa ana amfani da hulba don gyaran nono. Dalili kuwa shine, hulba na sanya fata da tsokar dake kewayen nonon mace su buɗe, hakan sai ya sa nonon ya ciko ɓulɓul abin sha’wa, musamman idan nonon ya kasance da girmansa amma ya kwanta.

Abubuwan da ake bukata sune; garin hulba da garin Shammar da kuma zuma.

Yadda za a hada.

 

 

Za a samu garin hulba da garin shammar. Ki ɗebi cikin ƙaramin cokalin guda daya (1) na garin hulbar sai a zuba cikin kofi mai tsafta da aka tanada , sannan a zuba garin shammar, shima cikin ƙaramin cokali guda, sai a gauraye su waje guda. Daga bisani a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara a kan garin hulba da na shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti 10 sai a tace da rariya, bayan an tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a sha.

 

 

Daga bisani sai a shafa man hulba ga nonon. Wajen shafawa akan nonon a tabbatar an murza man hulbar sosai akan nonon gaba daya yadda zai shiga fatar nonon da kyau. Za a sha wannan hadin sau biyu a rana, wato da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin hakanan za a shafa man hulbar a kan nonon, shi ma ya zama sau 2 kenan.

Yadda za ki gane maganin na amfani shine, ta hanyar jin nononki na kara nauyi, alamar ya fara cikowa kenan. Allah Ya sa mu dace,amin.

 

 

Karin Bayani: A inda mu ka ambaci amfanin hulba ga lafiyarmu, amma ba mu yi bayanin yadda za ayi amfani da ita ba, to mu na nufin mutum ya ke amfani da kwayoyin hulbar a abinci, ko kuma ya rinka yin shayinta ya na sha.

Idan a shayi mutum ke son amfani da hulba, sai ya ke shan kofi daya na shayin sau 2 a kullum, wato da safe da kuma dare.

.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button