Muƙabala Yanzu Yanzu Tsakanin Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi Da Prof Maqari Wa Kukewa Fatan Samun Nasara.

Muƙabala Yanzu Yanzu Tsakanin Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi Da Prof Maqari Wa Kukewa Fatan Samun Nasara.
TSARKI YA TABBATA GA ALLAH
Manyan Malamai dakarun Sunnah daga sassan Kasarnan suna kan hanya domin isowa garin Bauchin Yakubu saboda su taya Malam Idris fada akan taron dangin da ‘yan bidi’ah suka shirya masa
Akwai Kakanmu Malamin Sheikh Bello Yabo, wato Sheikh Musa Lukuwa da dalibansa daga Sokoto yanzu haka suna hanyar shigowa Bauchi
Akwai Malamai irinsu Sheikh Bashir Argungu daga jihar Kebbi, Sheikh Musa Asadussunnah daga Kaduna, Sheikh Sani Alkanawy daga Kano, Sheikh Baffa Hotoro daga Kano, Sheikh Abdallah Adam Kano, suna kan hanyar shigowa Bauchi wasu har sun isa sun fara gabatar da jawabi a daren nan
Yanzu haka Masallacin Dutsen Tanshi yayi cikar da babu masaka tsinke, gidan Malam ya cika da dakarun Sunnah wadanda suka shirya gwabza karo da mushrikai masu bautar shehunan karya
Wallahi kaunar Sunnah da Ahlussunnah ya kara karuwa a cikin zuciyata, sai da na zubar da hawaye saboda murna da farin ciki
AlhamdulilLah!
AlhamdulilLah!!
AlhamdulilLah!!!
Yaa Allah Ka taimaki Sunnah akan bidi’ah da shirka da tsafi
SANARWA DAGA KUNGIYAR IZALA AKAN MUKABALA DA MALAM IDRIS
Daga birnin Dutsen jihar Jigawa, inda shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala na jihar Bauchi bangaren Jos Sheikh Salihu Suleman Ningi yake gabatar da tafsirin Al-Qur’ani Maigirma yanzu haka, ya fitar da sanarwa akan mukabalar da hukumar shari’ah na jihar Bauchi ta shirya za’ayi da Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi
Sheikh Salihu Suleman Ningi yace babu hannun kungiyar Izala da yake jagoranci a cikin wannan zaman, kuma babu wani dan Izala da zai halarci zaman mukabala da Malam Idris akan abinda ya tabbata gaskiya ne a Sunnah
Malam yace duk wani dan Izala reshen Jos da aka gani gurin mukabalar ya je ne a kashin kansa ba da yawun kungiya ba, kamar yadda wasu suka fadawa Malam Idris cewa ‘yan Izalar Jos zasu shiga cikin ‘yan bidi’ah da zasuyi mukabala dashi, to ba gaskiya bane
Sannan a bangaren Izala reshen Kaduna jihar Bauchi, Sheikh Dr Ibrahim Disina yace Izalar Bauchi ta wakiltashi zasu halarci mukabalar domin su goyi bayan Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi
Gobe taron dangin ‘yan bidi’ah da zindikai a jihar Bauchi zasu kwashi kashinsu a tafin hannu da ikon Allah
Yaa Allah Ka daura gaskiya akan karya, Ka taimaki sunnah akan bidi’ah da shirka