Duk Wanda Ya Kara Taba Min Mahaifiya Sai Nayi Shara’ar Dashi Mawaki Rarara Ya Fusata Yanzu Yanzu…….

Duk Wanda Ya Kara Taba Min Mahaifiya Sai Nayi Shara’ar Dashi Mawaki Rarara Ya Fusata Yanzu Yanzu…….

Bincike akan Cutar Barin jiki (FAcson)da Hawan jini ko Yakai helcupter tashi Insha Allah.

 

Kwararran masani Akan Itatuwa da Maganin su, Malam Abu Marwana Andalusa, da Farfesa Elizabeth Renter sunyi tarayya akan bincike na 2015cewar duk duniya Nan Babu Maganin cutar Barin jiki (FAcson)da kuma yawan jini Kamar ganyan Ayaba.

 

Kuma F, Elizabeth Renter takara da cewa Alikitance Babu mgn ciwon Barin jiki (FAcson) sam.

 

Sannan akace To shi huran ayabar fa Wato wannan Mai Kamar masarar?

 

Sai sukace To shi kuma da za’a yanka shi Kashi 4 adafa Kashi 1 asha yau asha gobe to zainarkar da tsakuwar koda (Kidney stones) ayi fitsarin ta Nan take da yardar Allah asami lfy, inkuma anci Gaba Da sha Kamar na sati biyu to inda tsakuwar kodan ta kwanta wurin yayi miki To zaiwarke Gaba ɗaya Insha Allah.

 

Sai kusanar da Wasu suma Saboda Allah.

 

Ana tafasa shi ne akuma sha Kamar sau uku Arana Insha Allah za’a wuce wurin.

Y’an uwana zawarawa mata mafi yawa suna cikin masifar rayuwa😢😢

 

Kalubalen rayuwa da mata zawarawa suke fuskanta a wannan lokacin ya yi muni da yawa, daman kuma su ababen tausayi ne wadanda suke bukatar tausayawa da kuma taimakawa….

 

Kaso casa’in na y’an uwana mata zawara wadanda kaddara ta mayar da su gida inma mutuwar aure ko mutuwar miji sukan samu kansu a cikin wata sabuwar rayuwa tsukakkiya mai cike da fitintinu tun daga cikin gidajen iyaye ko na y’an uwa idan iyayenta sun mutu….

 

Na farko idan har mace ta zamo bazawara to a gidansu a kan barta da dawainiyar kula da kanta muddin iyayenta ba masu hali bane, ko tana sana’a ko batayi ba wanda zai damu da rayuwarta, idan tana da yara kuma akayi rashin sa’a mijin mutuwa ya yi ko kuma mugu ne haka za’a barta da dawainiyar yaran nan, sai y’an kadan da suke samun tallafi daga wajen wasu yan uwa da abokan arziki….

 

Irin wadannan masu yaran sukanyi wuyar samun namijin da zai aure su, domin da yawan maza yanzu ba su da tausayin dsukar dawainiyar kula da yaran wasu, wasu mazan kuma karfinsu bai kai su aure mace mai yara su cigaba da kulawa da dawainiyar yaran ba, hakan yakansa mace bazawara mai yara ta yanke kauna da aure……

 

Akwai wadanda kuma mijin ya mutu, iyayenta sun mutu kuma basu da gida sai na y’an uwa wallahi irin wadannan bala’in da suke samun kansu a ciki ko kare ba zaici ba, domin matsuguni guda daya da zasu zauna su samu kwanciyar hankali basu da shi, daman yan uwantaka a yau ya zamo sai “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”….

 

Hakan ke saka wata zamowa dillaliyar dole ko tallece tallace da neman kudi ta ko ina domin ta kama hayar inda zata zauna, idan mace ta samu kanta a cikin makura irin wannan y’an kalan suke tsira daga sharrin shaidan wajen fadawa fasikanci domin neman abin da za suci da yadda zasu zauna……

 

A bangaren mazan da suke zuwa neman zawarawa kaso mafi yawa iskanci ke kaisu, wasu sukanyi amfani da matsatsin da suke ciki su nemi yin fasikanci da su domin su basu kudi, wasu ka bazawarce zata takura ta nemi taimako don kula da kanta ko yaranta sai irin wadannan mazan su nemi sai sunyi iskanci da su…..

 

Wadannan bayani da nikeyi muku ba shaci fadi bane, ni ganau ne kuma jiyau kuma abokin shawarar mafi yawa daga cikin wadanda suke cikin irin wannan hali😭😭

 

Ina kiraga iyaye da makwafta da y’an uwa dan Allah mu rika jin tausayin mata zawarawa ko da ba y’an uwan mu na jini bane….

 

Sannan ku ma iyaye mata ku rika saka son junanku da tausayi da tsarkake zuciyarku kuna tausayawa y’an uwanku mata, domin kaso 90 na matsalolin mata zawarawa y’an uwansu mata ne sila……

 

Sannan ina jan hankalin y’an mata ku rike samarikan da suke sonku da aure, ku tsarkake zuciyarku kuyi aure domin ibadah da kokarin sakawa zuciyarku godiya da hakuri, zawarci masifa ce ku tambayi zawarawa….

 

Allah ya shirya mana al’umma ya yayewa kowa matsalarsa ameen.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button