Launukan ruwan da yake fita daga gaban Mace wanda yake da amfani da da marar amfani
Launukan ruwan da yake fita daga gaban Mace wanda yake da amfani da da marar amfani

Akwai launuka daban daban wadanda a dalilinsu ne ma ake iya rarrabe nau’o’in ruwan da ke da matsala da kuma mara matsala, gasu kamar haka :
1- White discharge (Vaginal Lubrication) : Akan sami dan farin ruwa kadan yana fita a gaban mace, dab da fara al’ada wannan ba matsala bace.
– Tsinkakken farin ruwa mara Kaikayi da yake fita a gaban mace Yana da amfani na tsaftace gaban mace da tabbatar da lafiyar gaban mace a kowanne lokaci.
Yadda halittun gaban mace take kullum iya kokorin kawar da matattun qwayoyin jiki da sauran qwayoyin cuta dake kwance a gabanta ko bakin mahaifa shi yasa ma cikin gaban mace ba bukatar dole dole a ansaka sabulu an wanketa.
2- Thick White : Farin ruwa mai yauki da kauri kamar majina mafi yawa ana ganin wannan bayan Al’ada da kwana 6 zuwa 10 wannan yana nuni ne da cewa lokacin Ovulation ne (Lokocin da mace tagama kyenkeshe koi) shi ma ba wata matsala ba ce.
3- Blushed deep pink: a likitance mance idan tagama Al’ada , kamar yadda mukai bayani a sama gaban mace tana tsaftace kanta , shine dalilin ganin wannan pink discharge bayan gama al’ada.
Kuma masu sabon ciki sukan yi wannan pink discharge alamace ta ciki shima ba matsala bace.
Kuma wani lokoci pink Vaginal discharge zai iya zama matsala idan yazo da alamomi kamat haka :
1- Karni
2- Kaikayi
3- Tsananin ciwon ciki.
4- Yellow – Green : Wannan itama wani lokocin takan faru ta dalilin matsalar abinci ko karancin wassu daga cikin sinadaran vitamin.
Shima idan yazo da alamomi kamar :
- Kaikayi
- Karni
- Ciwon ciki
Yakamata aga likita kai tsaye domin matsala ce.
5- Gray or dark discharge: wannan kai tsaye maatsala ce Wanda kwayar cutar bakteria take haifarwa tana zuwa da alamomi kamar haka :
- Kaikayi
- Ciwon ciki
- Karni
- Zapi
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta Bayanin akan Wannan maganin Zamu So Karben Ra’ayoyinku A sahen Mu Na Tsokaci.