Sheikh Kabiru Gombe Ya Goyi Bayan Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

Sheikh Kabiru Gombe Ya Goyi Bayan Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

AUREN KIFI DA TSUNTSU: HUKUNCIN AL-KAFA’AH A AURE.

 

Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta.

 

Watau ba soyayya ce aka hana a tsakanin Kifi da tsuntsu ba, amman dai kafin a ƙulla auren, ya kamata a gano matsalar inda za a zauna, domin rayuwar yau da gobe, la’akari da cewa shi dai Kifi ba ya iya rayuwa a bisa icce. Hakanan shi ma tsuntsu ba ya iya rayuwa a cikin ruwa…

 

A lokacin da na ke zaune a Maiduguri, shekara kamar 14 kenan da su ka wuce, ina da wani aboki da ke neman wata yarinya da aure. Wannan yarinyar kuma ta kasance ɗiyar ɗaya daga cikin manya manyan attajirai na wannan gari. Shi kuma aboki na ana iya sanya shi a matsayin middle-class. Shi ba talaka ba kuma shi ba mai kudi ba.

 

Dukkannin alamu sun tabbatar da cewa yarinyar nan ta na son aboki na da gaske. Kuma ta na da niyyar auren shi. To Amman shi kuma a kullun su ka hadu da ita, ya kan dawo da fargaba. Kullun ya je wurin ta, kara tsorata shi ta ke yi.

 

“Wai kai mallam ni na ga kullun ka dawo daga wurin yarinyar nan, maimakon in gan ka cikin annashuwa, sai in gan ka sukuku, duk kamar an zare ma ka lakka. Wai me ke faruwa ne.” Wata rana na tambaye shi.

 

Aboki na ya amsa ma ni da cewa “Abdullahi, ni fa a’lamarin yarinyar nan ya na ba ni tsoro. Kullun ba ta da wata hira daga labarin lokacin da ta raka wata yayar ta, Ingila, sai na zuwan su Dubai da wata auntyn ta. Ko kuma na zuwan su America ko Saudiyya. Ta dan rinka jefo labarin Abuja ma inda zan iya sa baki, ba ta yi. Yau ma labarin wata yar’uwar su ta ba ni, wadda aka aiko da private jet ya kwashi ‘yan zuwa suna. Sannan kullun mu ka hadu da ita, ko dai za ta kai ɗin ki, ko kuma ta amso din ki. Kuma wallahi duk irin manya manyan atamfofin nan ne da leshi ma su tsada. Anya kuwa ban ‘dauko Kano ba gammo ba'”

 

Wata rana na raka shi zance, sai ta ke ba mu labarin wata yar’uwar su da su ka rabu da mijin ta. Ta na ta zagin mijin ta na nuna tsananin rashin mutuncin shi. Sai na ce mata ni kam zan so jin irin rashin mutuncin shi. Sai ta ce ma ni to bari in ba ka misali:

 

“Wata rana su ka shirya za su je yawon shakatawa Dubai. Irin family outing din nan. To dama diyar su daya about one year. Sai matar ta ce a tafi da nany mai kula da baby. Shi kuma mijin ya ce gaskiya ba za a tafi da nany ba. So ya ke su tafi su uku kawai. Daga shi sai matar shi sai kuma babyn su. Saboda rashin mutunci irin na shi, hakanan ya bar ta ta yi ta wahala da baby a Dubai ita kadai” Mu ka hada ido da aboki na na ce “eh lallai bai kyauta ba kam”…lolsss

 

Bayan mun dawo gida ya ce ma ni to ka ga fa irin abinda na ke gaya ma ka. Na ce eh lallai kam na fahimci inda matsalar ta ke. Na ce ma shi wannan shine ake ce ma soyayyar Kifi da tsuntsu. Ya ce kamar yaya? Na ce ma shi ka san shi so a zuci ya ke. Ita kuma zuciya kowa ta gadama sai ta so. Ita kuma rayuwar aure rayuwa ce ta zahiri; rayuwa ce ta ƙeƙe da ƙeƙe ba ta zuci ba. Saboda haka idan Kifi da tsuntsu su ka ji su na son junan su, to babu laifi. Amman wace irin rayuwar za ayi? Kuma a ina za ayi ta?

 

Na ce yanzu dai ka fahimci irin rayuwar family din wannan yarinyar da kuma irin kallo da shirin da ta ke yi ma rayuwar ta ta nan gaba. Saboda haka za ka iya? Idan soyayya ta ja ku kun yi aure yanzu, me zai faru yau da gobe? Ka San kuma yau da gobe shine aure. Sannan kuma ka san ka na da wata matar wadda ita da dangin ta su na ma ka kallon Kai kamar wani hamshakin mai kudi ne. Ya ka ke ganin zaman zai kasance?

 

Daga karshe dai aboki na ya gamsu da cewar yarinyar nan ta fi karfin shi. Mu ka je tare kuma ya fada ma ta gaskiya. Ya kuma fada ma ta gaskiyar dalilin shi. Abun mamaki, yarinyar nan ta yi murmushi ta ce to Allah ya sa hakan shine ma fi alkhairi. Sannan ta ce bari in ba ku shawara don gaba. Ta ce ma na:

 

“Duk lokacin da mutun ya ki sayen nama mai kyau domin ya na ganin ya yi ma shi tsada, ya je ya sayi kafar sa, to lallai kam zai ji da kudin icce. Kila ma sai ya yi ciko”

 

To irin wannan banbancin matsayi a tsakanin ma’aurata wanda ka iya janyo matsaloli acan gaba bayan aure shi ne hukuncin ‘AL – KAFA’AH’ ya ke kokarin magancewa.

 

Al-kafa’ah na nufin compatibility in marriage. Watau ana iya cewa daidaito. Watau kowa ya auri tsarar shi, musamman mazaje. Ba a cika samun matsala ba idan mijin ne sama da mace wajen ilimi, arziki, danganta har ma da addini. Amman inda mace tafi mijin ta arziki, ilimi ko kana talaka tibis ka je ka auro diyar wani babban basarake ko hamshakin mai kudi, to Kai ma ka San fa akwai abinda zai biyo baya…..

 

Mazhabobin Hannafi, Shafi’i da Abu hanifa sun yarda da hukuncin Al-kafa’ah. Malikiyya ne su ka takaita akan hadisin manzon Allah inda ya ke cewa “idan kun yarda da addinin mutun da dabi’un shi, to ku ba shi aure…”

 

Amman a gaskiya akan samu irin wannan auren da ake yi a tsakanin ma’aurata ma su banbancin matsayi, inda macen kan fi mijin, daga baya kuma matsaloli su yi ta tasowa musanman daga bangaren mijin.. inda za ka ga mijin ya na jin cewa ta raina shi ko kuma dangin matar sun raina shi. Shi da dangin shi. Ko kuma ita matar ta ji duk ta takura sabida shiga wata sabuwar rayuwa wadda ba ta saba da ita ba a baya…

 

Wadansu kuma sai ka ga Allah ya daidai al’amarin sun zauna lafiya…

 

Allah ya yi ma na jagora a cikin dukkan al’amurran mu

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button