Yadda zaku hada maganin girman gaba, saurin kawowa, karfin gaba da kuzari lokacin saduwa
Yadda zaku hada maganin girman gaba, saurin kawowa, karfin gaba da kuzari lokacin saduwa

Ba shakka lallai wannan fa’ida ta kuke karantawa fa’ida ce wacce Al’umma da dama sukai amfani da ita kuma tayi musu tasiri wajen maganin sha’anin daya shafi jima’i.
Wannan fa’ida nayi tashar YouTube “MAIJALALAINI TV” sun cikekken bayani a kai kuma Alhamdulillah mutane da yawa sun tabbatar da cewa wannan fa’ida tana aiki sosai.
Hakan yasa naga ya dace mu rubuta ta ga sauran al’umma domin suma su samu su amfana da ita wajen magance abinda yake damun su bangaren zamantakewar aure.
Wannan fa’ida tana kara Sha’awa sannan tana kara ruwan maniy tana maganin saurarin inzali tana karawa Namiji sha’awa da kuzari da nishadi da jin dadi a lokacin saduwa da iyali.
Abubuwan da zaku nema domin ku hada maganin sune kamar haka.
(1) – Citta.
(2) – Ganyen Kuka.
(3) – Tafarnuwa.
(4) – Kanunfari.
Bayan kun nemo wadannan abubuwan ga yadda zaku hada maganin cikin sauki.
Da farko za’a samu ganyen Kuka guda 5 a shanya ya bushe a inuwa, sannan a samu garin Citta karamin chokali, sai garin Tafarnuwa karanin chokali da Kanunfari chokali 1.
Za’a hade su waje daya a dake su sosai, sai a rika diban rabin karamin chokali ana zubawa a ruwan shayi ba madara ana sha da safe da dare, amma za’a dauki kamar tsawon minti 30 kafin a kusanci iyali.
Za’a yi wannan hadin na tsawon sati 1 insha Allah za’a samu kuzari karfi da kuma dadewa ana jima’i da rashin saurin kwanciyar gaba.