Kisán Gílla Tsinanne Dan Jahannama Dama Dole Seka Mútu Bidion Yadda Mutane Suka Fusata Suka…

Kisán Gílla Tsinanne Dan Jahannama Dama Dole Seka Mútu Bidion Yadda Mutane Suka Fusata Suka…
YANDA MAI OLSA ZAI YI AZUMIN RAMADAN BA TARE DA WATA MATSALA BA.
————————————————–
Kamar yanda kuka sani, olsa kurji ne da ke samun tumbi ko hanjin dan adam.
Abubuwan da ke kawo olsa ko kuma suke iya tada OLSA su ne:
– shan maganin kashe ciwo ba akan ka’ida ba
– yawan cin abu mai yaji ko twanka
– yawan cin maiko
– yawan shan abu mai zafi
– yawan shan Lipton ko nescafe musamman wanda ba a saka madara ba.
– rashin cin abinci a cikin lokaci
– damuwa da yawan tunani.
MATAKAN DA YA KAMATA MAI OLSA YA DAUKA KAFIN WATAN AZUMI
——————————————————–
Ya kamata mai OLSA ya fara daukan matakai tun kafin shigowan watan Ramadan.
Daga cikin matakan da za’a iya dauka sun hada da:
– shan maganin OLSA a kan ka’ida
– shan magani sama da daya. Ma’ana Kada mutum ya sha magani kwara daya tilo domin OLSA na buƙatar magunguna biyu ko ukku
– shan maganin OLSA iya lokacin da a ka kayyade. Akwai maganin da ya kamata a sha har tsawon sati biyu, akwai na kwana goma. Duka ya kamata a shanye su.
– rage cin abin da ke iya tada olsa. Alal misali abu mai zafi, abu mai yaji, abu mai maiko dayawa.
MATAKAN DA YA KAMATA A DAUKA A CIKIN WATAN RAMADAN
—————————————————
– Yin sahur
– jinkirta sahur kamar yanda addini ya karantar
– kada a kwanta bayan cin abincin sahur, domin yin haka na iya tada OLSA
– shan maganin olsa bayan cin abincin sahur
– kada a ci abu mai yaji ko maiko ko lipton ko nescafe mara madara a lokacin sahur
– yin bude baki a cikin lokaci
– shan abu mai dan sanyi a lokacin bude baki
– cin dabino a lokacin bude baki
– shan maganin OLSA bayan bude baki
– kada a cika ciki sosai a zama daya bayan yin bude baki. A na son a ci abinci kadan kadan bayan mintuttuka ko awa
– shan kayan gona irin su ayaba. Kada a yi saurin shan laimu.
Idan an dauki wadannan matakan in shaa Allah za a samu sauƙin yin azumi musamman ga mai OLSA.
Akwai wadanda OLSA din su ya nada tsanani sosai ta yanda basa iya azumi. Ire-iren waɗannan mutane ya kamata su ga ma’aikatan lafiya.
Allah Ya sa mu dace.
Allah Ya gwada mana watan Ramadan mai albarka.
Dr Auwal Ahmed Musa
Asibiti A Tafin Hannun Ka
YADDA WASU MATA SUKA KWARE WAJEN JAN HANKALIN MAZAJEN SU
DOMIN SU RIKA DAWO MUSU GIDA DA WURI.
Wata mata tace, idan zan tashi miji na daga bacci dan yayi sallah sai na wanke hannuna da ruwan sanyi, na shafa turaren da yafi so a hannu na, sai in shafi dumin jikin shi in kai hannu na kusa da hancin shi. Wannan kamshin turaren sai ya sanya ya farka daga baccin shi koda ko ya kai kololuwa a bacci da minshari mai karfi. Kuma hakan na sa shi yayi gaggawan shigowa gida domin ya san ba zai dawo ya tarar da bacin rai ba.
Wata kuma tace, muna zaune kawai sai yace min zai je su ci abinci da abokan shi domin an gayyace su wajen cin abinci. Ko kina bukatar wani abu kafin in fita? Da yake ita mai wayau ce kuma ta san abokai in an hadu sai Allah, sai randa ta gan shi, kuma bata so tace mai kar ya dade kai tsaye. Sai tayi karaf tace mai eh dan Allah kar ka dade domin za’a dauke wuta. Sai yayi saurin juyowa gareta cikin mamaki yace mata wa ya fada miki wuta zai dauke? Tace ni na fada maka fitan ka kawai na sa gidan ko ina duhu ya rufe shi, amma da ka shigo sai ko ina ya haskaka komai yayi haske. Sai kawai yayi murmushi ya gane sakon da take bashi, ya tafi cike da shaukin dawowa gida ba tare da ya tsaya dogon fira da abokanan shi ba.
Ita ko wannan cewa tayi, lokacin da miji na ya gama shiri zai fita sai nace ya bude bakin shi ya rufe idon shi, sai ya rufe idon shi ya bude baki yana jiran yaji mai za’a mai, sai ta dakko cakulet da ta san yana so ta wurga mai a bakin shi. Bayan ya kai bakin kofa zai tafi sai ta sake ce mai haka. Yayi kasake yana jiran ya sake jin wannan cakuletin a bakin shi kawai sai yaji bakin ta cikin na shi ta sumbace shi ta ruga tana dariya tana daga mai hannu alamun bai-bai (Bye-Bye).
Nima nace muku BYE-BYE
Umar ibn Ibrahim.