Maganin matsalar kankancewar mazakuta da maganin girma da tsawon gaba

Maganin matsalar kankancewar mazakuta da maganin girma da tsawon gaba

Kankancewar zakari na nufin raguwar girman al’aura wato wani yanayi ne da al’aurar namiji baligi ke zama karama tamkar ta karamin yaro, ta shige ciki ko ta rage tsawo ko kauri a lokacin da take kwance ko a mike sabanin yanda take ada.

Wannan yanayi na faruwa ga mutum ne a lokacin da yake manyanta cikin rayuwarsa, a dabi’ance, hakan na faruwa ne ga mutane da shekarunsu na haifuwa suka kai 30 zuwa 40.

Amma duk da haka akan sami matasa da yawa wanda basu kai ga wadannan shekarun haifuwa ba masu fama da wannan matsalar.

Sai dai wasu da yawa daga cikin masu bada maganin gargajiyar hausa na ganin cewar matsalar kankancewar zakari matsala ce kai tsaye dake da alaka da zafi ko sanyin mara suke ikrari.

Kankancewar zakari dai matsala ce dake cima mazaje tuwo a ƙwarya musamman irin yanda wasu da yawa ke jin kimarsu da alfaharinsu na kasancewarsu maza na fuskantar ƙalubale.

Mutane a al’adun duniya da dama na ganin isasshen al’aurar namiji ita ce abin tunƙaho da fahari ga kowani mutum dake amsa sunansa namiji, kuma itace kimarsa ga ‘ya mace.

To saidai ƙanƙancewar zakari idan ba yawa tayi ba ba’a tunanin zata iya haddasa rashin gamsuwar jima’i tsakanin ma’aurata, akwai dalilai na lafiya da dama da zasu iya bada haske gameda ƙanƙancewar gaba.

Wasu dalilai na daban da ka iya haddasa kankancewar zakari ga matasa ko manya sun hada da.

1. Aiki ko tiyatar likita ga al’aura domin cire wani kullutun ciwon daji ko kansa daga al’aura (Prostate tumour/cancer surgery removal), yana iya haddasa kankancewar gaba bayan aikin.

2. Wata cuta (Peyronie’s disease) mai sauya sigar zakari, wato karkacewar zakari sosai da wuya ko zafi wajen yin jima’i. Yin tiyatar likita /ofereshin (surgery) domin maganin matsalar na iya haddasa ƙanƙancewar zakari.

3. Yanayin sanyi (temperature) . Idan sanyi ya yawaita fiye da yanda ya dace ga jiki to zakari zai iya noƙewa/ɓoyewa saboda ɗari. Hakan na hana gudanar jini da kyau a cikin al’aura, samun yanayi mai kyau da gumi zai iya maganin matsalar.

4. Sanya wandon ciki (under pants) wanda ya tsuke hantsa ko al’aura. Yana sanya karancin gudanar jini cikin al’aura wanda sakamakon hakan zai iya sanya zakari ya takura dalilin jini baya shiga ciki da kyau ta yanda zakar zai cika da jini ya kumboro (ya mike) a lokacin sha’awa ko jima’i. Wato jijiyoyin jinin basa aiki da kyau saboda takura.

5. Yawan fitar maniyyi sakamakon yawan yin istimna’i/ wasa da al’aura amma ba jima’i ba. Da zaran maniyyi ya fita daga jikin mutum jakar marainansa data sauko ƙasa kafin fitar maniyyi zata nade ta koma sama ta tsuke marainan biyu bayan fitar maniyyin.

A lokacin faruwar haka kuma zakari na shigewa shima ya koma gareji tare da marainan.

6. ƙiba: masu ƙiba da yawa na fama da ƙanƙancewar gaba domin kuwa tana sanya zakari ya shige ciki. Don haka, motsa jiki da rage ƙiba ta hanyar daya dace zaya iya maganin matsalar.

Barin shan taba ko giya, cin abinci mai kyau, motsa jiki, magani da shan wadataccen ruwa yanda ya dace zai taimaka sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button