Yau yan Tíjjaniyya sun shiga Uku a hannun baffa hotoro

Yau yan Tíjjaniyya sun shiga Uku a hannun baffa hotoro
Rayuwar Bazawara Na Cikin Hatsari
Babu abinda yafi mutuwar aure musiba da tashin hankali a rayuwar aure.
Duk lokacin da naga bazawara hankali na kan tashi saboda tashigo wata sabuwar rayuwa wacce bata saba da ita ba. Babbar musifar da bazawara zata fara fuskanta itace ɓullowar samari da zawarawa kamar ruwa, wanda kaso casa’in cikin ɗari ba don Allah suke sonta ba.
Da yawan su suna zuwa ne domin su tattaɓa jikin ta ko kuma suyi zina da ita domin biyan buƙatarsu, saboda su a tunanin su ai ta saba da kwanciyar aure yanzu kuma gashi ta rasa wannan damar.
A wannan lokacin ne za tayi ta cin karo da mazajen bariki tare da samarin zamani suna yi mata kyauta tare da bata kulawa kamar gaske daga nan kuma sai su hure mata kunne a shiga wani sabon babin na daban.
Allah ne kaɗai yasan adadin zawarawan da suka afkawa zinace-zinace tare da yawon bariki sakamakon yaudarar ƴaƴa maza. Da zarar ance ga bazawara nan to a wannan lokacin za kayi ta ganin gantalallun mazaje da mayaudaran samari kowa yana kai caffar sa wurin ta domin neman sa’a.
Da yawan zawarawa hankalin su kan gushe, karasa inda tunanin wasu ya tafi da wayonsu, saboda yadda shedan ke saurin yi musu huɗuba su karɓa.
Yakamata ƴan uwa na maza muji tsoron Allah saboda munfi matan laifi, sannan mu tuna da cewar zawarcin nan ƙaddarace zata iya faɗawa kan kowa, wasu mazajensu ke mutuwa wasu kuma ƙaddarar aure ce idan tazo sai an rabu.
Idan ka dauwama a lalata rayuwar zawarawa to yakamata kasani kaima fa kana da mata ko ƴa ko uwa ko ƙanwa kuma babu wacce bazata iya samun kanta a zawarci ba, kuma wallahi duk abinda ka yiwa ƴar wani ko uwar wani kaima sai an yiwa naka.
Mu tausayawa zawarawan nan mu basu kulawa ta musamman muma sai Ubangiji ya bamu kulawarsa, dukkan inda ƴa mace take komai ƙanƙantar ta uwace mu girmamata mu ɗora su akan madaidaitacciyar hanya, kada mu saka su kan hanyar da rayuwar su zata watse.
Muna roƙon Ubangiji ka kawowa zawarawa ɗauki, ka basu mazajen aure nagari ka tsaresu daga sharrin mazajen zamani
‘Yan uwana Mata masu daraja, zan gaya muku gaskiya mai tsada a kyauta saboda shigowar watan Azumi
Duk matar da ba ta bi mijinta sau da ƙafa ba, ba zai taɓa ririta ta yadda take so ba.
Mu maza, Allah ya halicce mu a ɗabi’ance da wata izza a kan iyalanmu irin wacce Allah yake ba wa shugabanni a kan mutanensu. Idan aka ce mana dole sai an yi wani abu, ko kuma muka buƙaci abinda Allah ya ce ayi mana a ka ƙi, to ko da an yi nasara ba za a mori nasarar a cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba.
Matar da ta fi kowa jin daɗi a duniya, ita ce wacce ta iya sarrafa miji da yi masa biyayya da haƙuri da shi. Sai dai idan namijin ba na ƙwarai ba ne.
Idan har ki ka ga ba ki zama mai biyayya ba, kuma miji ya ci gaba da lallaɓaki, to wallahi ɗayan uku ne: ko dai yana jiran lokacin da zai nuna miki matsayinki, ko asircacce ne, ko kuma dai kawai soko ne.
Ba ma son mata masu haɗa kafaɗa da mu.
Ba ma son mace marar godiya ga kaɗan ɗin da Allah ya hore mana.
Ba ma son mace mai yawan buri.
Ba ma son mata masu nuna son abin duniya, komi yawan abinda Allah ya hore mana da kuma yawan kyautarmu.
Na ga mata da yawa da suka yi wa mazaje tutsu da sunan haƙƙi, a ƙarshe sun rasa aurensu. Don babu yadda za ayi ki haɗa kafaɗa da mai ɗaukar ɗawainiyar rayuwarki, kamar yadda mutum bai isa ya ja da Ogansa a wurin aiki ba.
Na ga mata da suka rabu da miji saboda su mallaki abin duniya. Sun samu abin duniyar, amma farin ciki bai samu ba.
Babu yadda za ayi mace ta ɗauki irin ɗawainiyoyin da maza suke ɗauka ba tare da abin yana damunta ba. Komai wadatarta.
Shi kuwa namiji, kullum farin ciki yake idan ya sauke nauyin iyali.
Maza da mata ba ɗaya ba ne. Allah ma ya bambanta. Kuma duk wanda ya saɓa yadda Allah ya tsara, a ƙarshe sai abin ya dame shi.
Ki yi ƙoƙarin sarrafa namiji daidai yadda ki ka iya kawai, amma kada ki taɓa tunanin ba zai ƙara aure ba. Duk daɗin bakin da namiji zai miki fa, yana son ƙara aure sai dai idan bai samu dama ba, ko kuma irin masu damar amma masu tsananin tsoron talaucin nan.
©️Sulaiman Badamasi