Yadda zaku hada maganin kankancewar gaba sadidan

Yadda zaku hada maganin kankancewar gaba sadidan

Kowanne lokaci burin mu shine taimakawa ‘yan uwa da hanyoyin da zasu bi domin su magance matsalar da take damun su.

A yau ma kamar kullum nazo muku da wannan fa’ida ta musamman domin magance matsala wacce ake samun ta tsakanin ma’aurata ta bangaren Namiji.

Wanda baya iya gamsar da matar sa a yayin saduwa, ko wanda gaban sa baya da karfi ko wanda yake saurin zuwan kai.

To ga wannan fa’idar ayi kokari ayi amfani da ita domin a magance wannan damuwa sabida gudun samun matsala a zamantakewar aure.

Da farko zaka samu wadan nan abubuwa kamar haka.

(1) – Man shanu.

(2) – Garin kammun.

Kammun ana samun sa a wajen masu Islamic chemist baya wahala, idan aka same shi za’a dake shi sosai sai yayi laushi a tankade shi.

Sai a samu man shanu amma danye za’a kwaba wannan garin kammun din da man shanu amma kar yayi kauri da yawa.

Bayan an kwaba su gaba daya ga yadda za’a yi amfani da su wajan sha.

Yadda ake sha shine, ana diban karamin chokali a rika zubawa a nono ko kunu ko yogut ana sha da safe da kuma dare, ayi tsawon sayi 2 ana wannan hadin insha Allah za’a sami yadda ake bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button