Allahu Akbar Miji Da Mata Sun Mutu Kwana Biyu Tsakani, Sun Bar Yaransu Kanana Guda Biyu
Allahu Akbar Miji Da Mata Sun Mutu Kwana Biyu Tsakani, Sun Bar Yaransu Kanana Guda Biyu

Dr Barde Luka Yelwa, wani malamin Kwalejin koyan malanta dake garin Gashua a jihar Yobe ya rasa ransa ranar Alhamis da ya gabata, bayan ya samu bugun zuciya a asibitin da yake jinyar matarsa wacce ba ta da lafiya.
Kwana biyu bayan rasuwar mijin nata, ita ma ta rasu a ranar Asabar, inda yau Litinin za a yi jana’izar su biyun a ikkilisiya ta ECWA GOODNEWS dake garin Potiskum a jihar Yobe.
Sun mutu sun bar yara biyu, mace yar shekara biyar da kuma namiji dan shekara biyu.
Wannan bayin Allah muna fatan Allah yaji kansu da rahama kuma yasa aljanna ce ma komar su muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani.
Daga Suleiman Dauda