Kalli hadin maganin karfin Azzakari mai saukin haɗawa

Kalli hadin maganin karfin Azzakari mai saukin

Jaraba Mace Da Wadannan Abubuwan Domin Tabbatar Da Matsayinka Da Dacewar Aurenta:

 

SHARE 💞

#Tsangayarmalamtonga

 

Akwai wasu Mahimman abubuwan da zaka yi cikin sauki domin fahimtar idan mace tana sonka da gaske.

 

 

1: Yi Mata Alkawarin Da Bazaka Cika Ba- ba tare da ta nema ba. Kawai kayi mata alkawarin wani abu dakasan zata so.

 

Bayan kayi mata alkawarin kayi banza da zancen kada ka sake mata zancen abun ka ga yadda zata dauki ka.

 

Wasu mata a irin wannan yanayin zasu soma kunci da matsawa namiji akan wannan abun kullum sai sun tambaya wanda zai nuna maka daman wani abu ne a ranta ba kai ba.

 

Amma idan mace na sonka da gaske ko zancen ba zata sake maka ba muddin ba kai bane ka sake tado da maganar ba. Ta haka zaka fahimci cewa kaine a ranta ba wannan abun ba.

 

2: Ka Ce Mata Babu Ko Bazaka Iya Ba: Idan ta tambayi wani abun datasan kafi karfinsa ce mata babu ko kuma ba zaka iya bata ba.

 

Jira kaga yadda zata maida maka martani bayan wannan furucin.

 

Wasu matan daga wannan lokacin soyayyar ya kare. Wata kuwa ta rika mitar ka gaza mata abunda take so.

Kana fahintar irin wannan martanin daga gareta fita batunta.

 

3: Rage Daukar Wayarta- Idan ta kiraka kada kayi saurin dauka, kuma kada ka kira miss call dinta cikin lokaci.

Mace mai sonka zatayi kokarin sanin laifin da tayi ba a daukar wayarta. Tare da bada hakuri tun ma kamin a sanar da ita laifinta.

Amma wacce ba soyayyar gaskiya bane a tare da ita, zata daina kira ko turo sakon text. Ko kuma ta tura kalamai marasa kyau a gareka.

 

4: Hanata Zuwa Inda Kake- Idan wacce take zuwa wajen aikinka ce ko inda kake kasuwanci taka mata burki wajen amfani da kalmami mara dadi. Misali “bana so na sake ganinki a nan” . Ko “ki daina zuwa inda nake”.

 

Kana fadin haka ka kula da fuskarta domin ganin yanayin da zata shiga.

Mace mai sonka kana fadamata hakan kishinta zai motsa. Zata nemi sanin abunda kake kokarin boye mata. Zata so sanin laifinta.

 

Amma idan daman lashe money ce bakar magana zata maida maka. Ko kuma ta bar wajen cikin kunci da alwashin ba zata sake zuwa ba.

 

5:Kaita Sayayya- Dauki wacce zaka aura bayan kasan kana da wadatar kudi a jikinka zuwa katin sayya Mall.

Mata marasa hankali da daba idan ka kaisu kace su dauki abunda suke so anan zaka fahimci mace ta aure da mace ta holewa.

 

Wata idan ta rika kwaso kaya har na wanda ba zai mafeneta ba ko bata ma taba amfani da shi ba zata dauka saboda samun banza.

 

Mace mai hankali ba zata dauki wani abun da zai wuce na yan kudi kadan ba.

Haka nan idan ka kai ta yawan cin abinci. Kaga tana odar abincin da bata ci a gidansu saboda Samun banza fita harkarta.

 

Macen aure kana kaita cin abinci zata yi odan abunda tasan zata cinye, ba wanda zata ce a kawo mata ba sannan tayi cukali biyu tace ya isheta. Mata suna dauka wani abun burgewa ne basusan tanan namiji na fahintar mace wacce batada tausayi ba.

 

Ya kamata mata da dama su fahimci cewa, maza masu natsuwa da neman matar auren data dace sunada hanyoyin da suke gwada wacce zasu aura da yawa. Da fatan zaki zama mai hankali da wayo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button