Ga Sauki Gareku Mata: Matan da suke jin zafi a lokacin da ake jima’i dasu, Ga hanyar da zasu magance wannan lamarin

Ga Sauki Gareku Mata: Matan da suke jin zafi a lokacin da ake jima'i dasu, Ga hanyar da zasu magance wannan lamarin

Da yawa yawan mutane (musamman mata), suna korafi akan zafi da suke ji a lokacin jima’i ko kuma lokacin da ba’a jima’i dasu. Wannan babbar damuwa ce da mafi yawan lokaci kan addabi ni’imar mace, da kuma hanata sukuni sosai.

Zafin yana faruwa ne sakamakon wasu abubuwan da kan iya haifarwa hakan, misali anyi matsi wanda zai takura farjin mace, ko kuma dalilin wasu cututtuka dake damun farjin mace, da dai sauran su.

Idan mace tana fama da wannan al’amari, akwai abubuwan da ake yi don ganin an rabu dashi na har abada. Wadannan kuwa sun hada da neman magani, kula da tsaftar jiki (musamman farji), neman shawarwari na masana, da dukkan matakai na kare kai.

Da zarar anbi dukkan sharuddan kariya ga Kai, akwai amanna da kuma kyakkyawan fata akan za’a samu sakamako wanda ake bukata.

Duk mai fama da wannan matsalan zata nemi kayan hadi kamar haka:

Garin Ganyen kabewa.
Garin Ganyen zogale.
Garin Hulba
Garin Majigi.
Man kadanya

Yadda Zaki Hada Wannan Sirri Shine :

Zaki samu kayan hadin sai ki hada su guri guda ki kwaba da man kadanya sai ki dunga shafawa sau uku a rana, duk shafawa sai ki wanke da ruwan dumi zakiyi mamaki kwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button