Sirrin maza wanda ya kamata kowanne namiji ya sani,domin gamsar da iyalin sa hadi na Musamman

Sirrin maza wanda ya kamata kowanne namiji ya sani,domin gamsar da iyalin sa hadi na Musamman

Hakika namiji yana da wani sirrin Wanda ba kowacce mace ta San wadannan sirrin ba Sai wacce Allah ya sanar da ita, shi namiji ya kasance Mai tsanani son karairaya, rangwada, kissa,shagwaba, da kalaman soyayya, duk macen data San wadannan kuma take aikatasu hakika zata zama tauraruwa a zuciyar mijinta.

Babu KO shakka wadannan kam Na Daga cikin abubuwa mafi muhimmanci dake taka muhimmiyar rawa wajen sace zuciyar namiji ,ya kasance kin tanadi wani suna Na musamman da Zaki dinga kiran mijinki dashi kamar

 

● sweety

● honey

● darling

● Abin kaunata

● farin cikin rai Na.

 

Magana ta gaskiya a wannan fannin a nan ne aka yiwa matan hausawa nisa , don da yawa sune basu dauki hakan a wani Abu Mai muhimmanci dake Iya jefa tsantsar sonki a zuciyar mijinki ba.

 

Dole a matsayin ki Na macen da ke son ta mallaki mijinta saifa ta dage wajen Iya kalaman soyayya don sune masu kwantarwa da namiji hankali koda kuwa an bata masa rai KO hankalinsa ya tashi.

 

Sannnan yana Daga cikin namiji ki Iya gabatar da zahirin soyayya, hakika tsakaninki da mijinki bafa jin kunya, ki Saki jikinki ki nuna masa soyayya, domin duk wani hade-hade da manne-manne da zakiyi idan Har baki Iya kalaman soyayya ba da ita kanta soyayyar to gaskiya da sauranki.

 

Misali idan ya kasance Ku biyu ne akayi sa’a baki iyaba KO kuma kice kina jin kunya Amma ita abokiyar zamanki ta Iya Sai kiga yana zumudi a duk lokacin da akace yaune ranar kwananta.

 

Sannan Daga cikin sirrin namiji a wajen jima’i karki zauna shirim baki tabuka komai, ya kasance kema kanki kina gabatar da salo Na shagwaba da duk wani yanayi da zai Iya Saki nuna masa cewa kefa kina jin dadin wannan jima’i dashi.

 

* ABINCINKI MU MAGANIN MU*

 

AYABA

 

cin ayaba yana Kara yawan maniyyi.

yana motsa sha’awa jima’i.

yana maganin ulcer ( gymbon ciki )

yana gyaran magudanar fitsari.

idan akaci ayaba biyu a yini KO fiye da haka yana maganin amfani wajen maganin Tafi.

Mai fama da ciwon makogwaro ya yawaita cin ayaba.

yana maganin ciwon kirji.

tana maganin kyasfi, Sai a kwaba ta da ruwan Khal a rinka shafawa a kyasfin.

tana maganin hawan jini su yawaita cin ayaba.

A samu bawon ayaba busasshe Sai a daka a hada da Zuma da nono a rinka sha, tana maganin ulcer.

 

*TUMATUR *

 

tumatur yana magani ciwon sugar.

yana maganin karacin jini za’a markada shi a sa sukari a rinka sha.

domin mikewar nono Na mace, ya tsaya car a mike ba zubewa, to a samu za’atar a hada da koren tumatur a jajjaga a rinka shafe nono da shi, sannan a samu rigar nono a sa duk lokacin da aka sa.

 

*✤ MATSE GABA ✤*

 

matan albarka ga wani sirrin, Zaki samu.

 

✤ ya’yan hulba.

✤ tafarnuwa

✤ garin bagaruwa

✤ kanunfari

 

Ki dafa shi ki Kama ruwa dashi, zakiyi Na kwana biyu.

 

● MASU NEMAN RAGE ( TUMBI ) TEBA? ●

 

Duk lokacin da aka ci abinci, a rinka raka abinci da lemon

 

Shan lemon tsamiya, bayan magani da tsamiya ke yi ,itama tana kone kitse da gyaran jiki da rage teba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button