Kada Ka Sake Kayi Aure Idan Kanada Irin Wadannan Matsalolin

Kada Ka Sake Kayi Aure Idan Kanada Irin Wadannan Matsalolin

ZAMANTAKEWAR AURE GA MA’AURATA DARASI NA MUSAMMAN.

 

Shi dai aure ibada ne. A cikin sa akwai dadi akwai kuma wahala. Wani lokacin yana zuwa da jarabawa kamar dai yadda sauran aiyuka na ibada suke.

 

Wasu suna yiwa aure fahimta na daban, wasu ma auren suke ba tare da sun fahimce shi auren ba.

 

Akwai kuma masu yiwa auren wani irin kallon. Wanda da wannan kallon suke shiga harkar aure har ma suyi. Irin wadannan maza ne ko mata, basa jimawa cikin auren sai su rabu.

 

Don haka muddin kana yiwa aure irin wannann kallon ko kana sone kayi aure saboda wadannan dalilan to gara ma kada kayi.
1: Wasu suna yin aure ne saboda sun ga abokansu ko wasu na kusa da sun yi. Hakan yasa suma sai kawai suyi.

 

Duk wanda zai yi aure da irin wannan tunanin ba tare da ya shirya ba zai iya fuskantar matsala a nan gaba.

 

2: Saboda Suruntu mutane wasu sai kawai su ce zasu yi aure. Kada ka bari surutun masu surutu ya tunzura yin aure baka shirya ba. Domin su wadannan da suke surutun sune kuma zasu ci gaba da wani surutun na ka kasa rike matar.

 

Don haka aure Kada ka yi shi sai ka shirya masa.

 

3: Wasu kuma na yin aure ne da tunanin zasu hole. Sam aure ya wuce wannan. Domin akwai holewa akwai kuma horarwa. Don haka ka shirya wa dukkannin su muddin kana son zaman aurenka ya inganta.

 

4: Wasu suna yin aure ne saboda tsaro. Irin wadannan mutane musamman ma mazajen da suke zuwa wasu karshen Turai su zauna.

 

 

 

Sai su samu ‘yar kasa su aure ba saboda Allah ba sai domin garkuwa da ita wajen samun takardun zama a Kasar. Bayan wani dan lokacin da samun biyan bukata sai kuma su nemi raba auren ko kuma su ɓace ma a daina ganin su.

 

Idan ka san bada gaske zaka yi aure ba kada kayi wasa da zuciyar wanda ya nuna maka so.

 

5: Akwai masu auren saboda gudun fushin iyaye amma ba domin suna son yin auren ba. Irin hakan idan ya faru sai kuma su rika cutar da wanda suka aura.

 

Bin iyaye ibada ne akan hanyar Allah. Haka Shima aure ibada ne. Don haka duk wanda kayi wasa da shi cikin biyu kana iya fuskantar fushin Allah

 

Yana da kyau ka zauna da iyayen ka ko wasu na kusa dasu idan kana da dalilin ka na rashin son auren a yanzu sai ka fahimtar dasu maimakon kayi kuma kaje kana cin mutuncin aure.

 

Wadannan yalayen ba wai ya tsaya ga maza kadai ba. Har mata suna yin aure saboda irin wadannan dalilan daga bisani ko dai su zauna cikin azabar miji ko kuma su kasa hakuri su fito.

 

Abunda ya kamata kowa ya gane aure ba ayinsa da wasa ko kuma da garaje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button