Sai mai aure kukan dadi, yadda zakasa kowata mace ta kawo ruwa

Sai mai aure kukan dadi, yadda zakasa kowata mace ta kawo ruwa

Sai mai aure kukan dadi, yadda zakasa kowata mace ta kawo ruwa

HA’INCIN DAKE CIKIN MAGUNGUNAN ƘARA GIRMAN NONUWA DA MAZAUNAI DA AKE CE WA “NATURAL” NE
Kina so ki ƙara girman ababen halittar ki sabida ki burge mai gida ko ki ƙara farin jini wajen samari.

Sai dai kin sani cewa akwai magungunan da su ke da illa In mutum ya ce su zai yi amfani dasu, magunguna kamar su sha ka fashe (Dexamethasone), muna ta fadakarwa akan illolin shan shi cewa yana iya kawo hawan jini, ciwon suga, ciwon Gaɓɓai, kumburin jiki da matsalar koda.

A dalilin haka sai kika ce ke kin hakura da amfani da sha ka fashe, za ki samu maganin gargajiya wanda yake PURELY NATURAL, watau tsantsan na gargajiya ne. Sai ki ka siyo

Zuman ƙara nonuwa da mazaunai
Garin ƙara ƙiba
Haɗin ƙara ƙiba da sauran nau’in magunguna.

Mata da yawa suna tambaya na, shin amfani da waɗan nan magungunan na da illa ko bashi dashi?

Bincike na sirri ya bayyana mana wani abin tada hankali. Yawanci masu iƙirarin cewa maganin su purely herbal/natural ne ƙarya suke.

Misali:
Wata mata na siyar da:
Garin kunu na gyaɗa da riɗi mai ƙara ciccikowan hips da nonuwa da ni’ima ga mace.

Ashe ba gyaɗa da riɗi kaɗai take sa sawa a cikin kayan haɗin na ta ba. Tana siyo SHA KA FASHE (DEXAMETHASONE) ta haɗa a ciki takai niƙa. (Kamar yadda za’a gani a hotunan nan).

Yanzu ke da ke kula da lafiyar ki, kike gujewa amfani da sha ka fashe saboda illolin shi amma kike siyan irin Wannan magungunan, ashe an gudu ba’a tsira ba.

Jama’a muyi taka tsantsan da irin magungunan da muke sha, mu tuna wasu fa kuɗin kawai suke so ba ruwansu da lafiyar jama’a.

Sunana Pharm. Musa A Bello, fadakarwa da ilmantar wa game da lafiyar ku shi ne nawa, sai kuyi share da like domin mutanen mu su amfana su kare lafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button