Allahu Akhbar An Kammala Jana’izar Uwa Da Yarta Yan Garin Dutsin-ma ta Jahar Katsina da Suka Rasu Sakamakon Haɗarin Mota.

Allahu Akhbar An Kammala Jana’izar Uwa Da Yarta Yan Garin Dutsin-ma ta Jahar Katsina da Suka Rasu Sakamakon Haɗarin Mota.

Allahu Akhbar An Kammala Jana’izar Uwa Da Yarta Yan Garin Dutsin-ma ta Jahar Katsina da Suka Rasu Sakamakon Haɗarin Mota.

Muna cikin jimami sanar da ku rasuwar daya daga cikin mabiya wannan Jarida mai albarka Hajiya Wasila Amadu wacce take amfani da sunan ( Umm Sajjad) sun rasu ita da mahaifiyarta a kan hanyarsu ta dawowa daga Jahar Jigawa wajen wata ta’aziyya.

Lamarin da ya faru bayan sallah Mangariba wajen Kauyan Sha’iskawa hanyar Kankiya, inda nan take ita ta mahaifiyarta suka ce ga Garinku nan, wasu daga cikin motar sun samu karaya a kafa shi kuma direban ya bugu a gurare daban daban na jikinsa

Wakilinmu ya halarci jana’izarsu a Garin na Dutsanma tare da kawo kadan daga cikin nasihar da wani Malami ya gabatar kafin yin addu’a, ya fara cewa ina kiran Al’umma “akan kowama ga Allah yana mai cewa wadannan bayin Allah lafiyarsu kalau jiya amma yau gamu mun rakosu gidansu na gaskiya,wallahi mun sani watarana mu za’a kawo ko kai ko ni, wallahi kowa ya an kawo shi nan ko ya shirya ko bai shirya ba.

Idan maganar shiri ake yi wadannan bayin Alah basu zuwa inda zasu tarar da aljalinsu, amma babu yadda suka Iya gashi yanzu zamu tafi mu barsu.

Ya cigaba da cewa nasan hajiya Wasila tare muka Makaranta bata da Abokin gardama balle fada, duk inda zaka kwatatanta Mutum wajen kirki da Mu’amula to ta kai, muna fatan Allah Ya gafarta masu, mu sani kuma mu kiyaye wannan yana tare gamu, kuma daga mu sai aikinmu kamar yadda makiya da masoyan wadannan bayin Allah basu kara ganinsu har abada.

A karshe Munayi Masu Addu’a Allah Yaji Kansu da rahama Idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani ameen.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button