SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI DA ILLOLIN SU!!! KWAYA ko MAGANI

SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI DA ILLOLIN SU!!!
KWAYA ko MAGANI

shine duk abinda idan ya shiga jikin dan Adan yake kawo chanjin yanayi cikin kwakwalwa ko jikinsa ta kowani fanni, misali kota hanya sha ne, shafawa ne, shaqawa ne kokuma ta yin allura.

MIYAGUN SHAYE SHAYEN:

– Shan maganin da doka ta hana amfani dashi.

– Shan Magani berkete batare da izinin likita ba.

– Wuce umurnin likita wajen shan kwayoyi.

– Shan abubuwan da addinin Musulunci ya haramta.

DALILAN DA SUKE SA JAMA’A SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI;

1) Jahilci
2) Matsalolin Rayuwa
3) Al’adu
4) Hada hadan siyasa
5) Hurda da abokan banza
6) Sakacin iyaye wajen tsawata wa yara
7) Yanayin wurin zama
8) Aikin karfi (leburanci)
9) Samun kwayoyin cikin sauqi
Da sauran su….

WASU DAGA CIKIN MIYAGUN KWAYOYIN DA AKAFI AMFANI DASU;

1) Tabar wiwi (Indian Hemp)
2) Sholisho
3) Hodar Aljanu (cocaine)
4) D5 (Valium, Diazepam, Exol 5)
5) Taramol (tramadol)
6) Kashin kadangare
7) Afarci kasa (pemoline Tablet)
8) Hodar Iblis (heroine)
9) Maganin mura da akesha ba bisa ka’ida ba kaman, (Emzolynn, Tutolyn/Codein, Benalyn/codeine etc)

MATAKAI NA SOMA SHAYE SHAYE:

– GWAJI; wannan shine mataki na farko wanda mutum zai soma kusantar ko soma mu’amala da masu shaye shaye harta kaishi ga soma tabawa kadan.

– MASU SHAYE SHAYEN GANIN DAMA;

Wannan matakin mai shaye shayen yanasha ne lokacin da yaga dama, baya saya da kudin sa, sai ya samu na banza kona bati.

MASU SHAYESHAYE AKAI AKAI;

wannan shine matakin kama shaye shaye gadan gadan, ko yanada kudi ko babu sai yasha.

DOGARA KAN SHAYE SHAYE;

wanda yakai wannan matakin matakin bazai iya komai ba sai yasha idan baisha kwaya ba bazai zauna lafiya ba, wanda yakai wannan matakin kullum zaka sameshi cikin maye, a wannan matakin yana iya sata domin ya sayi kwaya.

ALAMOMIN DA AKE GANE MAI SHAYE SHAYE:

1) Rashin nutsuwa
2) Halin lalaci
3) Yawan fushi da rashin hakuri
4) Rashin ladabi, rashin Kunya
5) Yawan abokai daban daban
6) Amfani da bakin gilashi
7) Yawan arangama da Jami’an tsaro
8) Samun mutun da miyagun kwayoyi
9) Yawan yawo da ruwa ko lemon kwalba. Da sauran su…

ILLOLIN SHAYE SHAYE:

1) Yawan fadace fadace
2) Rashin nutsuwa a koda yaushe.
3) Talauci
4) Kora daga wurin aiki ko makaranta
5) Yana kawo hatsari ga wanda sukasha suke yin tukin mota ko babur.
6) Yana kawo ciwon huhu
7) Yana kawo ciwon hauka
8) Yawan tunani mai tsanani da muni.
9) Yana kawo lalacewan mazakuta.
10) Yana kawo cutan Tsida (HIV/AIDS) saboda idan hankali ya gushe ana jima’I berkete, sannan akwai masu amfani da allura waje yin maye.

11) Yana kawo lalaci, yadda mai shaye shaye baya iya’yin komai sai yasha kwaya.

KADAN DAGA HANYOYIN DA ZA’ABI WURIN MAGANCE SHAYE SHAYEN;

1) Ya zama wajibi iyaye su tashi tsaye wurin kula da tarbiyan yara da matasa, sannan su dinga kula da harkokin yaran su na yau da kullum, su kuma kula da irin abokan da yaran su suke hurda dasu.

2) Dole ne iyaye su kula da irin mutanen da suke shiga da fita a cikin gidajen su, su kuma kula da irin mutanen da iyalan su suke hurda dasu (mata ko maza), saboda yanzu matan aure sun shiga harkan shaye shaye sosai.

3) Dole ne Sarakuna da Malaman Addini su tashi tsaye wurin tsawatarwa da fadakar da Al’ummah bisa illan shayeshaye ta mahangar addini da rayuwa.

4) Dole ne kuma Al’umma su bada hadin kai wurin taimakawa Jami’an tsaro da jami’an yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi wurin gudanar da ayyukan su!

5) Makarantu da kungiyoyin addini da kungiyoyin sakai, da dukkan Al’ummah dole ne su tashi gadan gadan wurin taima kawa gwamnati da al’umma wurin wayar da kan jama’ah game da illolin shaye shaye.

Daga karshe ina kira ga dukkan Al’umma da su bada gudun mawan su wurin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi domin kaucewa fadawan Al’ummar mu cikin halaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button