Masha Allah Jarumi Hamisu Breaker Yayi Auren Sirri Tun Watannin Bakwai Da Suka Wuce
Masha Allah Jarumi Hamisu Breaker Yayi Auren Sirri Tun Watannin Bakwai Da Suka Wuce

A Kishin Kishin Labarin Da Ya Zo Mana Yanzu Shine Hamisu Breaker Yayi Auren Sirri Tun Watannin Bakwai Da Suka Gabata Kamar Yadda Muka Samu Wani Bayani Daga Tashar Kudin Shahara Dake Kan Manhajar YouTube
Tashar Sun Bayyana Abubuwa Guda Uku Da Suka Sa Mutane Suka Gaskaka Maganar Auren Inda A Farko Wani Na Kusa Da Hamisu Ya Bayyana Cewar Mawakin Ya Sayi Sabuwar Mota Inda Ya Bawa Matarsa Tsohuwar Motartasa Wadda Hakan Yasa Muke Tunanin Daman Hamisu Yayi Aure
Na Biyu Kuma Kan Maganar Tattaunawar Hadiza Gabon Tayi Da Rukayya mousa Kan Saurayin Mawaki Da Ya Yaudaraita Wadda Sanadiyyar Hakan Yasa Mutane Yin Tsokaci Cewar Shida Ya Rigada Yayi Aure Miye Na Maganar Ya Yaudareta Wadda Mutane Da Yawa Ne Suka Fada Hakan
Sai Abu Na Uku Da Shafin Dokin Karfe Suka Wallafa Wadda Mu Mun Yadda Da Shafin Yana Kawo Labari Na Gaskiya Inda Suka Bayyana Cewar
DA DUMI-DUMI: Shin Ko Kun San Cewa Mawaki Hamisu Breaker Ya Yi Aure Watanni Bakwai Da Su Ka Wuce ?
DAGÀ Shafin Dokin Karfe TV Labarin da ke shigowa Ofishinmu na Jaridar Dokin Karfe TV da d’umi-dumi yanzu-yanzu, wata majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa fitaccen mawakin Hausa, Hamisu Breaker Dorayi ya yi aure cikin sirri tsawon watanni bakwai da su ka wuce.
Hamisu Breaker, babban mawaki ne mai rere wakokin soyayya masu ratsa zuciya cikin harshen Hausa, wanda ko da a yan kwanakin da su ka gabata an yi ta cece-ku-ce akansa biyo bayan wasu kalamai da abokiyar sana’arsa wacce ta ke taka rawa cikin wakensa, Rakiya Musa ta yi cikin hira da Hadiza Gabon inda wasu ke zargin cewa da Hamisu Breaker din ta ke irin yadda ta siffanta tsananin soyayyar da ta ke yi wa wani mutum tun kafin ya samu daukaka.
A binciken da Jaridar Dokin Karfe TV ta gudanar ta gano cewa tabbas Hamisu Breaker ya yi aure a wani yanayi mai kama da sirri tayadda hatta abokan sana’arsa a masana’antar Kannywood ba kowa ne ya sani da auren ba sai yan kalilan.
Shin ko mai ya sa babban jarumin mawaki kamar Breaker ya yi aure cikin sarri duk da irin daukaka da shuhurar da ya ke da ita ?, Shin masu karatu mai za ku ce?
Da Fatan In HakannYa Zamo Gaskiya Allah Ya Sanya Da Alkairi Ya Basu Zaman Lafiya.